An Gaya Wa Kotun Koli Wanda Za Ta Ayyana Ya Yi Nasara Tsakanin Gwamna Dauda Lawal da Matawalle

An Gaya Wa Kotun Koli Wanda Za Ta Ayyana Ya Yi Nasara Tsakanin Gwamna Dauda Lawal da Matawalle

  • Wata ƙungiyar haɗin gwiwa ta dage cewa hukuncin kotun daukaka ƙara da ta kori Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara bai yi adalci ba
  • A hukuncin da kotun daukaka ƙara ta yanke, ta soke zaben Lawal tare da bayar da umarnin sake zaɓe a ƙananan hukumomi uku: Maradun, Birnin-Magaji da Bukkuyum
  • Sai dai ƙungiyar mai suna ‘Northern Initiative for Peace and Economic Development’ ta ce hukuncin ya saɓa wa tsarin dimokuradiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Gusau, jihar Zamfara - Wata ƙungiya mai suna Northern Initiative for Peace and Economic Development, ta buƙaci kotun ƙoli ta yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan zaɓen gwamnan jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Akwai lauje cikin nadi: Atiku ya ki sakin bayanan takardun karatunsa bayan ya fallasa Shugaba Tinubu

A wani taron manema labarai kwanan nan a birnin Jos na jihar Plateau, shugaban ƙungiyar Abel Jilemsam, ya buƙaci kotun ƙoli da ta mutunta ƴancin da jama’a ke da shi a Zamfara.

An bukaci kotun koli ta yi adalci a shari'ar Dauda da Matawalle
An shawarci kotun koli ta yi adalci a shari'ar zaben gwamnan Zamfara Hoto: Governor Bello Matawalle, Dauda Lawal
Asali: Facebook

'Kada ku lalata ƙa'idojin dimokuradiyya' - ƙungiyar ga kotu

A cewarsa, hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige gwamna Lawal “ya saɓa da ra'ayin mutanen Zamfara" kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Vanguard ta kuma lura da matsayar ƙungiyar ta cimma kan hukuncin shari'ar zaɓen na Zamfara.

Jilemsam ya ce:

"Al’ummar jihar Zamfara sun yi amfani da ƴancinsu na dimokuradiyya, kuma dole ne a ji su a kuma girmama su."
Duk wani ƙoƙarin ɓata sahihancin wannan zaɓen ba wai kawai zai lalata tsarin dimokuraɗiyya ba ne a Najeriya, amma har ma da sanya yardar da mutane suke da ita kan zaɓe ta dusashe."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka yi wa jami'an NDLEA kwanton bauna, bidiyo ya bayyana

"Muna kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumomin zaɓe da ɓangaren, su tabbatar an yi hukunci bana son kai ba yayin da aka garzaya kotun ƙoli kan taƙaddamar da ta taso daga hukuncin kotun ɗaukaka ƙara."

Kotu Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Dauda

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Zamfara, ta tabbatar da nasarar Gwamna Dauda Lawal na jam'iyyar PDP.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da Bello Matawalle da jam'iyyar APC suka shigar suna ƙalubalantar nasarar Gwamna Dauda a zaɓen na ranar 18, ga watan Maris 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng