Akwai Lauje Cikin Nadi: Atiku Ya Ki Sakin Bayanan Takardun Karatunsa Bayan Ya Fallasa Shugaba Tinubu

Akwai Lauje Cikin Nadi: Atiku Ya Ki Sakin Bayanan Takardun Karatunsa Bayan Ya Fallasa Shugaba Tinubu

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya ƙi sakin bayanan karatunsa
  • Atiku ya yi ƙoƙari sanya wa a soke takarar Bola Tinubu ta hanyar tura lauyoyi su tilastawa jami’ar jihar Chicago (CSU) ta saki bayanan karatun Tinubu
  • Jaridar Premium Times ta buƙaci takardun karatun Atiku, amma rahotanni sun ce ya kasa ba su sati bakwai da samun takardar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, da ƙin fitar da bayanan karatun sa.

A wani yunƙuri na ganin kotu ta haramtawa shugaban ƙasa Bola Tinubu takara, Atiku ya aika da lauyoyinsa zuwa Amurka domin tilastawa jami’ar jihar Chicago (CSU) a bisa doka ta saki bayanan karatunsa.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Kogi: Dan takarar APM ya kai karar Ododo kotu? Gaskiya ta bayyyana

Atiku ya ki sakin takardun karatunsa
Atiku ya ki sakin takardun karatunsa bayan fallasa Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sai dai dan siyasar haifaffen jihar Adamawa ya kasa fitar da nasa bayanan karatun kamar yadda Premium Times ta buƙata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya ƙi sakin takardun karatunsa

Jaridar ta yanar gizo ta ce ta buƙaci jigon PDP da ya ba da kwafin takardun shaidar karatun da ya samu tun daga firamare har zuwa jami'a, ciki har da takardar shaidar digiri na biyu, kamar yadda ya yi ikirari a cikin takardar da ya mika wa hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a lokacin da ya tsaya takarar zaɓen shugaban ƙasa na 2019 da 2023

Sai dai rahotanni sun ce Atiku ya ƙi sakin takardun sati bakwai bayan da aka aike masa da wasiƙa a kan haka.

Jaridar ta ce ta aike da kwafin duka asalin wasikar da kuma tunasarwa zuwa gidan Atiku da ke unguwar highbrow Asokoro da ofishin yaɗa labaransa inda aka karɓe su kuma aka amince da su.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan bindiga suka yi wa jami'an NDLEA kwanton bauna, bidiyo ya bayyana

"Ƴan aiken mu sun mayar da shaidar isar da wasiƙar zuwa hedkwatarmu." A cewar jaridar tare da raba kwafin wasiƙar.

Yadda Atiku yayi gwagwarmaya don samun bayanan CSU na Tinubu

Bayan ya zo na biyu a zaben shugaban kasa na 2023, Atiku ya garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen.

Daga cikin su ƙorafe-ƙorafensa, ya zargi Tinubu, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da yin jabun satifiket daga jami’ar jihar Chicago.

Ya ƙalubalanci sahihancin kwafin takardar shaidar CSU da shugaban ƙasa Tinubu ya baiwa INEC har ma ya cigaba da neman wasu takardu bayan jami’ar ta tabbatar da cewa shugaban ya kammala karatu a makarantar.

Duk da haka, Atiku wanda ya je har Amurka a yunƙurin fallasa Shugaba Tinubu ya ki fitar da nasa bayanan na karatunsa.

Akwai Kuskure a Takardun Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ƙoli ta hango kuskure a takardun karatun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a jami'ar CSU.

Mai shari’a John Okoro, jagoran kotun mai alƙalai mutum bakwai da ke sauraron buƙatar da Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP, ya shigar kan nasarar da Tinubu ya samu, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng