Atiku da Ɗangote Sun Lale Naira 3bn Sun Baiwa Ɗan Takarar Gwamna a Arewa? Gaskiya Ta Yi Halinta
- Sanata Dino Melaye ya musanta jita-jitar cewa Atiku da Ɗangote sun ba shi N3bn kafin zaben gwamnan jihar Kogi
- Melaye, ɗan takarar PDP a zaben da aka yi ranar 11 ga watan Nuwamba, ya ce rahoton kanzon kurege ne babu kanshin gaskiya
- Ya kuma bayyana wasu darussa da a cewarsa ya koye su a lokacin zaɓen jihar Kogi da aka kammala
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a inuwar PDP a zaben da aka yi kwanan nan, Sanata Dino Melaye, ya yi bayani kan kuɗin da ake zargin ya karɓa.
Sanata Melaye ya musata raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya samu makuɗan kuɗi har N3bn daga wurin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Aliko Ɗangote.
Ya bayyana haka ne a wurin wata liyafa da aka shirya domin girmama shi a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan takarar wanda ya sha ƙasa, ya ce wasu bara gurbi masu neman kauda hankalin jama'a ne suka kirkiri wannan jita-jitar da nufin ɓata wa tawagar kamfe dinsa suna.
Da yake musanta zargin gaba ɗaya, Melaye ya byyana rade-radin cewa ya karbi N1bn daga Atiku da kuma N2bn daga Dangote a matsayin "labarin karya" da "maciya amana" suka ƙirƙira.
Na koyi darussa a zaben Kogi - Melaye
Tsohon dan majalisar tarayya ya kuma zayyana darussa guda uku da ya koya daga tsayawa takara a zaɓen Kogi da aka yi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Ya ce:
"Ɗaya daga cikin darussan da na koya shi ne, shiyyar gabas sun gane ba zasu iya kafa gwamna su kaɗai ba, dole sai sun haɗa kai sauran shiyyoyin kafin su cimma nasara."
Dan takarar gwamnan na PDP ya kuma ƙara da cewa akwai bukatar hadin kai tsakanin mambobin PDP a jihar musamman a Kogi ta Yamma idan ana son jam'iyyar ta iya cin zaɓe.
Dalilin da ya sa gwamnan Ondo da zai yi murabus ba
A wani rahoton na daban Har yanzu ana ta takaddama kan yanayin rashin lafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.
Yayin da wasu ke ganin ya kamata ya yi murabus saboda rashin lafiya, Gwamnatin Ondo ta ce gwamna na yin aikinsa.
Asali: Legit.ng