Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Da Ke Neman a Tsige Sanatan PDP

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Da Ke Neman a Tsige Sanatan PDP

  • Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da karar da Hon. Darlington Nwokocha na jam'iyyar LP ya shigar kan Sanatan PDP, Austin Akobundu
  • Kotun daukaka karar ta umurci dan takarar LP, Nwokocha da ya biya Sanata Akobundu naira miliyan 5
  • Nwokocha ya tunkari Kotun Daukaka Kara domin ta sake duba tare da soke tsige shi da aka yi daga majalisar dokokin tarayya ta kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke zama a Abuja ta tabbatar da hukuncinta da ya ayyana Sanata Austin Akobundu na PDP a matsayin mai wakiltan yankin Abia ta tsakiya.

Kotun Daukaka Karar ta yi watsi da karar da Hon. Darlington Nwokocha na jam'iyyar LP, ya shigar na neman ta janye hukuncinta na farko inda ta ayyana Sanata Akobundu a matsayin ainahin wanda ya lashe zaben majalisar dokokin tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Kotu ta ci tarar gwamnan Arewa miliyan 500 kan zargin take hakkin dan takara a zabe

Kotun daukaka kara ta tabbatar da sanatan PDP
Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Da Ke Neman a Tsige Sanatan PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jam'iyyar PDP ce ta sanar da hakan a wata wallafa da ta yi a shafinta na X @OfficialPDPNig a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta umurci dan takarar jam’iyyar LP, Nwokocha da ya biya Sanata Akobundu zunzurutun kudi har Naira miliyan 5.

Majalisa ta rantsar da sanatan PDP

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa majalisar Dattawa ta rantsar da Austin Akobundu na jam'iyyar PDP da ke wakiltar Abia ta Tsakiya a Majalisar.

Legit Hausa ta ruwaito cewa kotun daukaka kara ta bai wa Akobundu nasara bayan ya kalubalanci nasarar dan jam'iyyar LP.

Kotun ta kwace kujerar dan takarar na jam'iyyar LP, Darlington Nwokocha saboda kura-kurai da aka samu a yayin gudanar da zabe.

PDP ta zargi APC da kulla-kulla

A gefe guda, mun kuma ji a baya cewa babban Jam’iyyar hamayya ta PDP ta fara kokawa cewa akwai kutun-kutun da ake yi domin karbe mata kujera a majalisar dattawa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jawabi ya fito daga ofishin Sakataren yada labaran PDP, ana zargin APC da kitsa yadda za a hana Austin Akobundu shiga ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng