An Fada Ma Kotun Koli Wanda Za Ta Sanar Ya Ci Zabe Tsakanin PDP da APC a Filato

An Fada Ma Kotun Koli Wanda Za Ta Sanar Ya Ci Zabe Tsakanin PDP da APC a Filato

  • Wasu gamayyar kungiyoyi sun nage cewa babu adalci a hukuncin kotun daukaka kara da ya tsige gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang
  • A hukuncinta na watan Nuwamba, kotun daukaka karar ta soke zaben Mutfwang sannan ta nemi INECD ta ba dan takarar APC, Nentanwe Yilwatda Goshwe takardar shaidar cin zabe
  • Sai dai kuna, kungiyoyin arewa sun ce hukuncin ya yi karo da tsarin Damokradiyya wanda a kansa ne aka kafa Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jos, jihar Plateau - Wata kungiyar arewa mai suna 'Northern Initiative for Peace and Economic Development', ta bukaci Kotun Koli da ta jingine hukuncin kotun daukaka kara kan zaben gwamnan jihar Filato.

Abel Jilemsam, shugaban kungiyar, ya yi jawabi ga manema labarai a garin Jos, jihar Filato kwanan nan sannan ya bukaci Kotun Koli da ta mutunta zabin al'ummar Filato.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa yayin da aka zargi Tinubu da haddasa rikicin siyasa a Kano

APC na neman raba gwamnan Filato da kujerarsa
An Fada Ma Kotun Koli Wanda Za Ta Sanar Ya Ci Zabe Tsakanin PDP da APC a Filato Hoto: Daser David, Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Filato: 'Ki yi adalci': Kungiyoyin arewa ga kotu

A cewarsa, hukuncin kotun daukaka kara da ya tsige Gwamna Mutfwang ya saba muradin al'ummar Filato, jaridar Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Blueprint ma ta ruwaito matsayin kungiyoyin arewan.

Jilemsam ya ce:

"Mutanen jihar Filato sun aiwatar da yancinsu na damokradiyya, kuma ya zama dole a ji kokensu sannan a mutunta shi."
"Kokarin bata murde wadannan zabubbuka ba wai kawai kawo cikas ga tsarin dimokradiyyar da Najeriya ke bisa kai bane, har ma da kawar da yardar jama'a kan tsarin zaben.
"Muna kira ga masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumomin zabe da kuma bangaren shari'a, da su tabbatar da cikakken hukunci ba tare da son zuciya ba, yayin da muka tunkari Kotun Koli kan takaddamar da ta taso daga hukuncin kotun daukaka kara."

Kara karanta wannan

Kungiyoyin arewa sun bayyana hukuncin da ya kamata kotun koli ta yanke kan zaɓen gwamnoni 3

Gwamnan Filato na ware Musulmi?

A wani labarin, mun ji cewa al'ummar Musulmi a jihar Plateau sun karyata jita-jitar cewa Gwamna Cale Muftwang na jihar Plateau na nuna musu wariya.

Musulman su ka ce Gwamna Caleb na iya bakin kokarinsa wurin tabbatar da adalci a tsakninsu da Kiristoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng