A Karshe, Jam'iyyar PDP Ta Fara Ɗaukar Matakan Farfaɗowa Daga Bugun da Ta Sha a Zaben 2023
- Babbar jam'iyyar adawa ta fara ɗaukar matakan magance matsalolin cikin gida da suka haɗa mambobinta faɗa
- A taron kwamitin gudanarwa (NWC) na ƙasa, PDP ta umarci 'ya'yanta su janye ƙararrakin da suka shigar a gaban kotu
- Rigingimun cikin gida na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ake ganin sun kassara PDP a zaben da ya wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Peoples Democratic Party (PDP) ta ƙasa ta umarci dukkan mambobi su gaggauta janye duk wata ƙara ta suka shigar a gaban kotu kan rikicin cikin gida.
Babbar jam'iyyar adawar ta bada wannan umarni ne ranar Talata, 5 ga watan Disamba, 2023 a Abuja a wani yunƙuri na warware duk wani rikicin cikin gida.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa umarnin na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran PDP na ƙasa, Mista Debo Ologunagba, ya fitar bayan taron NWC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP, Ologunagba, ya ce kwamitin ya bada umarnin janye ƙararrakin ne bayan nazarin halin da jam'iyya ke ciki.
Meyasa PDP ta ɗauki wannan matakin?
Ya kara da cewa umarnin da NWC ya bayar ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP da aka yi wa garambawul a shekarar 2017.
Haka nan kuma ya ce janye ƙararrakin na faɗa da juna tsakanin 'ya'yan PDP zai taimaka wajen tabbatar da hadin kai da sulhu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kakakin PDP ya ce:
"Kwamitin NWC ya roƙi daukacin jagororinn jam’iyyar, masu ruwa da tsaki da mambobi su hada kan su wuri ɗaya, su ci gaba da yaɗa manufofin PDP, jam’iyyar dimokuradiyya ta gaskiya."
Ologunagba ya kara da bayanin cewa NWC ya kuma yi nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin da aka kafa domin nadin babban darakta-janar na Cibiyar Dimokuradiyya ta PDP.
Idan baku manta ba, rikicin cikin gida na ɗaya daga cikin dalilan da ake hasashen sun jawo wa PDP faɗuwa a babban zaɓen 2023.
Zamu tabbata an yi adalici - Sanatan Kaduna
A wani rahoton na daban Sanata Sunday Marshall Katung ya ce zasu tabbata an yi wa mutanen da harin bam ɗin sojoji ya shafa adalci.
Katung, Sanata mai wakiltar Kaduna ta kudu ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu a kauyen Tudun Biri.
Asali: Legit.ng