APC: Gwamna Diri Na Bayelsa Ya Matsawa EFCC Ta Kama Ministan Buhari
- Jam'iyyar APC reshen Bayelsa ta zargi Gwamna Douye Diri da matsawa EFCC lamba ta kama tsohon minista, Timipre Sylva
- Mai magana da yawun APC na jihar, Buokoribo, ya ce Diri na kulla wannan makirci ne domin ya hango zai rasa kujerarsa a kotu
- Sylva, ƙaramin ministan man fetur a gwamnatin Muhammadu Buhari ya sha kaye hannun Diri a zaben 11 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Jam'iyyar APC reshen jihar Bayelsa ta yi zargin cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) na fuskantar matsin lamba kan ta kama Timipre Sylva.
APC ta ce tana zargin Gwamna Douye Diri da matsa wa EFCC ta kama tsohon ƙaramin ministan man fetur kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu kan wasu dalilai.
Mai magana da yawun APC a jihar Bayelsa, Doifie Buokoribo, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Litinin, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sylva ya nemi zama gwamnan Bayelsa a ranar 11 ga watan Nuwamba a inuwar APC yayin da Gwamna Diri, ya nemi tazarce a inuwar am’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Hukumar zabe ta ƙasa (INEC) ta ayyana Diri a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu kuri'u mafiya rinjaye 175,196 yayin da Sylva, tsohon minista ya zo na biyu da ƙuri'u 110,108.
A halin yanzu, tsohon ministan ya kalubalanci nasarar Gwamna Diri na PDP a kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna.
Meyasa Diri ya matsa a kama Sylva?
Kakakin APC a jihar, Mista Buokoribo, ya ce Diri na tunzura EFCC ta kama Sylva tare da gurfanar da shi gaban kuliya domin ya hana shi kwato haƙƙinsa kotun zabe.
A rahoton Daily Post, Buokoribo ya ce:
"Muna sane da yunkurin sanata Diri a hukumar yaƙi da masu cin hanci da rashawa EFCC ta kasa da nufin daukar nauyin tuhume-tuhumen da aka kirkira a kan Sylva."
"Haka kuma mun san matsin lamba da yake yi wa jami’an EFCC don su kama shi kana su gurfanar da shi a gaban kuliya bisa wasu tuhume-tuhume na karya dangane da lokacin da ya riƙe karamin ministan albarkatun man fetur.”
NNPP ta fayyace gaskiya kan Abba da Kwankwaso
A wani rahoton Wasu korarrun mambobin NNPP na neman sake jawo wa Gwamna Abba Kabur Yusuf da Kwankwaso matsala.
Sun fito suna yaɗa cewa Abba ba ɗan NNPP bane kuma an kori Kwankwaso, amma jam'iyyar ta fito ta bayyana gaskiya.
Asali: Legit.ng