An Nemi Kotun Koli Ta Tsige Shugaba Tinubu Yayin da Aka Fara Wata Sabuwar Shari’a
- An nemi Kotun Koli ta tsige Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa kundin dokar da ya ce 'Lis Pendens'
- Jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP) ta bayyana cewa kundin dokar Lis Pendens ya ayyana zaben shugaban kasar 2023 matsayin 'haramtacce'
- Kodinetan jam'iyyar na kasa, Alhaji Ibrahim, a cikin wata sanarwa ya kalubalanci Tinubu kan karbar rantsuwar kama aiki a watan Mayu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP) ta nemi Kotun Koli ta tsige shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Jam'iyyar HDP da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019, Chief Ambrose Owuru, ta ce ya zama wajibi a tsige Tinubu kan karbar rantsuwar kama aiki matsayin shugaban kasa.
Lis Pendens ya haramtawa Tinubu zama shugaban kasa - HDP
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar ta ce tun da shugaban kasar na sane da cewa akwai shari'ar da aka daukaka ta yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa na 2023, bai kamata ya kama aiki ba, kamar yadda ThisDay ta rawaito.
Kodinetan jam'iyyar na kasa, Alhaji Anwal Ibrahim ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja, a ranar Litinin 4 ga watan Disamba.
Jam'iyyar adawar ta yi ikirarin cewa kudin dokar 'Lis Penden', ya yi nuni kan cewa Tinubu bai cancanci darewa kujerar shugaban kasar Najeriya ba, Legit ta ruwaito.
Me ya sa Kotun Koli za ta tsige Tinubu daga shugaban kasa?
Ta ce kundin dokar Lis Pendens ya ayyana zaben shugaban kasa da aka gudanar 2023 matsayin 'haramtacce' abin watsarwa.
A cewar sanarwar, a ranar 18 ga watan Mayu, Tinubu ya samu izinin Kotun Koli na shiga cikin shari'ar da ake yi da Owuru.
Ibrahim ya ce da Tinubu ya sani da bai gabatar da kansa har aka rantsar da shi matsayin shugaban kasa ba, tunda har yanzu ana nan ana gudanar da shari'arwacce ta hada da Buhari.
Majalisar tarayya ta gudanar da taron jin ra'ayi kan kasafin 2024
A wani labarin na daban, majalisar wakilan tarayya ta shirya wani taron jin ra'ayoyin jama'a kan kasafin kudin shekarar 2024 da shugaban kasa Tinubu ya gabatar.
Kwamitin kasafin kudi karkashin ofishin kakakin majalisar ya gudanar da taron a babban birnin tarayya Abuja, kuma ya samu halartar manyan mutane, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng