Tinubu Ko Buhari: Bulaliyar Majalisa, Ndume, Ya Bayyana Wanda Ya Fi, Ya Bai Wa Kowa Maki
- Ali Ndume, sanata mai wakiltar Borno ta kudu, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tafi ta magabacinsa, Muhammadu Buhari
- Ndume, wanda shine Bulaliyar Majalisar Dattawa, ya ce Tinubu na bibiyar ayyukan da ya bayar, sabanin Buhari, wanda masu madafun iko a gwamnatinsa ke canja akalar ayyukan
- Sanatan ya ce wasu mutane sun fi morar gwamnatin Tinubu, amma duk da haka yana kokarin kaucewa kura-kuren da Buhari ya tafka
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Ali Ndume, Bulaliyar Majalisar Dattawa kuma mai wakiltar Kudancin Borno a Majalisar, ya bayyana bambancin da ke tsakanin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta Shugaba Muhammadu Buhari da ta shude.
Da yake jawabi a shirin "Politics Today" na gidan talabijin na Channels, sanatan ya ce ba Buhari ne ke gudanar da gwamnatinsa ba, saboda baya bibiyar ayyukan da ya bai wa wanda ya bai wa mukamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndume ya bayyana wanda suka ci amanar gwamnatin Buhari
Ndume ya bayyana cewar akwai bara gurbi a gwamnatin Buhari, kuma ko Buhari ya yadda da haka a kwanakin baya.
"Yanzu shugaban kasa na sanya ido. Ya na sanya ido, ba kamar tsohon shugaban kasa ba. Shi zai sa ka aiki. Ba zai sake bibiya ba.
"Wannan shine matsalar, kuma shi (Buhari) ya san haka. Wannan shine kuskuren da Buhari ya yi. Sai kwanan nan ya fito ya ke bayanin akwai bara-gurbi a gwamnatinsa fiye da masu son cigaba."
Ndume ya yaba da kokarin Tinubu
Ndume, wanda jigo ne a jam'iyyar APC ya ce matakin Shugaba Tinubu na korar dansa daga wajen taron Majalisar Zartarwa abin yabawa ne, musamman da wasu da yawa baza su iya haka ba.
Sai dai, sanatan ya kara da cewa akwai wasu masu rike da madafun iko da ke kokarin amfani da dama amma saboda yana kokarin kaucewa kuskure irin na Buhari ya isa ya karya su kuma a samu gyara.
Kalli bidiyon tattaunawar a nan:
Asali: Legit.ng