Bai San Ana Yi Ba, Sanatan APC Ya Fadi Babban Kuskuren Buhari a Shekaru 8
- Mohammed Ali Ndume ya haska bambancin da yake gani akwai tsakanin Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu
- Sanatan kudancin Borno ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kewaye kan shi da barayin gwamnati a mulkinsa
- Ali Ndume ya nuna shi kuwa Bola Tinubu kar yake, ya san duk abin da yake faruwa a gwamnatinsa, akasin zamanin magajinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Mohammed Ali Ndume ya ce akwai wasu mutane da handama da sata kurum su ka sa gaba a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Sanata Mohammed Ali Ndume ya yi wannan magana ne da aka yi hira da shi a tashar Channels game da kasafin kudin shekarar 2024.
‘Dan majalisar yake cewa an samu barayi da yawa a lokacin da Muhammadu Buhari ya ke karagar mulki tsakanin shekarar 2015 da 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marabar Muhammadu Buhari da Bola Tinubu
Mohammed Ali Ndume ya nuna akwai bambanci tsakanin shugaba mai-ci Bola Ahmed Tinubu da magajin na sa, Muhammadu Buhari.
Vanguard ta ce Sanatan na Borno ya ce salon mulkin Bola Tinubu ya tabbatar da shi yake rike akalar gwamnatinsa, abin da ya ce an rasa da.
Wasu su na zargin akwai wasu miyagu da aka yi a gwamnatin baya, wadanda su ka rika juya madafan iko duk da ba su aka zaba a ofis ba.
Abin da Ndume ya fada a kan Buhari, Tinubu
Shugaban kasar yanzu shi yake rike da madafan iko. Wani abu guda game da shi kenan. Wasu su na ganin Tinubu ya cika karfa-karfa.
Gaskiyar maganar shi ne ya sha bam-bam da tsohon shugaban kasarmu. Shi sai ya bada aiki kurum amma ba zai sake neman ka ba.
Kuskuren da shugaba Muhammadu Buhari ya yi kenan. A karshe ya amsa cewa ya tara barayi fiye da wadanda su ke da asalin kishi."
- Muhammad Ali Ndume
Bola Tinubu ya fara taka burki
Sanatan ya ce ya san da zaman barayi a lokacin Buhari, amma daga abin da Tinubu ya yi wa ‘dansa, Ndume ya ce za a fahimci bambancin.
Shugaba Tinubu ya hana Seyi Tinubu da duk wanda ba a gayyata ba zuwa taron gwamnati.
Shugaba Tinubu da kasafin kudin 2024
A jiya aka samu labari Hon Yusuf Shitu Galambi ya ce Shugaba Bola Tinubu ya karanta masu lissafe-lissafen kasafin kudi ne kurum.
'Dan majalisar yake cewa babu cikakken bayani da gundarin yadda kasafin kowace ma'aikata yake a kundin da aka kai majalisar tarayya.
Asali: Legit.ng