Binciken da Gwamnatin Buhari ke yi ya tona asirin barayi
- Gwamnatin Shugaba Buhari na binciken ma'aikatu 33 na Kasar
- Daga cikin wadanda aka tasa gaba akwai irin su Hukumar JAMB
- Yanzu da dama na Ma'aikatan JAMB sun shiga hannun Hukuma
Gwamnatin Shugaba Buhari tun a baya can ta dauki niyyar binciken wasu manyan ma'ikatun Gwamnatin Tarayya har 33 domin gano irin badakalar sa aka tafka a lokacin Gwamnatin baya inda aka saci kusan sama da Naira Biliyan 450.
Daga cikin ma'aikatan da ake bincike akwai WAEC da JAMB wanda yanzu haka an fara jin gaskiyar abin da su ka faru. Sannan kuma akwai irin su Hukumar NIMASA, da Hukumar FAAN da ke kula da tashar jirgi da kuma Jami'ar nan ta NOUN me je ka da kwarin ka.
KU KARANTA: Yadda Hameed Ali ya tatsowa Najeriya Miliyoyin kudi a tashi guda
Dama dai Gwamnati ta fara gano wasu kudin da aka karkatar a maimakon a maidawa asusun Gwamnatin kasa. Yanzu haka a Hukumar JAMB, binciken ya kai wasu sun fara bayyana yadda wadannan kudi su ka salwanta bayan an damke su.
Ku na da labari cewa wata ma'aikaciyar JAMB ta bayyana cewa wani maciji ne ya hadiye kudin da aka tara har Miliyan 36. Wasu kuma dai sun nuna cewa katin da ake amfani da shi domin jarrabawar sun kone. Yanzu haka dai ana ta bincike domin gano gaskiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng