Wasu Hadimai Sun Yi Jabun Sa Hannun Gwamnan APC Don Sace Kuɗi? Gaskiya Ta Bayyana
- Gwamnatin jihar Ondo ta yi fatali da jita-jitar cewa an haɗa jabun sa hannun Gwamna Rotimi Akeredolu wajen wawure kuɗin baitul mali
- Misis Bamidele Ademola-Olateju, kwamishinar yaɗa labarai da wayar da kai ta Ondo ce ta bayyana gaskiya ranar Alhamis
- Ta ce har yanzu Gwamnan yana duba takardun da ya kamata da sauran ayyukan da suka rataya a wuyansa na shugabancin Ondo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Gwamnatin jihar Ondo ta musanta zargin cewa wasu ɗaiɗaikun mutane sun kwaikwayi sa hannun Gwamna Rotimi Akeredolu domin wawure kuɗin baitul mali.
Kwamishinar yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Misis Bamidele Ademola-Olateju ce ta karyata ikirarin da ake yaɗawa ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba.
Ta karyata jita-jitar ne yayin hira da ƴan jarida jim kaɗan bayan fitowa daga taron majalisar zartarwa ta jihar Ondo a Akure, wanda ya shafe sama da sa'o'i biyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Vanguard ta tattaro, taron ya gudana karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa, kuma shi ne na farko tun bayan ɓarkewar rikicin siyasa.
Hakan na zuwa ne bayan Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani, ya sasanta Gwamna Akeredolu da mataimakinsa.
Menene gaskiyar takardun da ake yaɗawa?
Kwamishinar yaɗa labaran ta yi bayanin cewa Gwamnan yana iya yin aiki har yanzu kana ta yi watsi da jita-jitar cewa an saci sa hannunsa a wasu takardu.
A kalamanta ta ce:
"Babu wanda ya yi jabun sa hannun mai girma gwamna. Batutuwan da aka tattauna a taron sun maida hankali ne kan maslahar da aka yi yayin ganawa da shugaban ƙasa ranar Jumu'a."
"Mun tattauna matsayar da aka cimma domin tabbatar da zaman lafiya kama daga kowa ya tsaya matsayinsa, mataimakin gwamna ya sa hannu kan takardar murabus da sauransu."
Gwamna Obaseki ya yi magana kan takarar Shaibu
A wani rahoton kuma A karshe, Gwamna Obaseki ya maida martani kan takarar mataimakin gwamna, Philip Shuaibu a zaben da ke tafe a jihar Edo 2024.
Gwamnan ya bayyana cewa miliyoyin mutane ne zasu yanke wanda zai ɗaga tutar PDP a zaben gwamnan jihar Edo na gaba.
Asali: Legit.ng