Mambobi Sun Zaɓi Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa da Mataimaki
- Majalisar dokokokin jihar Nasarawa ta zabi sabon kakakin majalisa da mataimakinsa a zaman ranar Alhamis
- Wannan na zuwa ne ƙasa da awanni 48 bayan kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tsige tsohin kakakin majalisar, Ibrahim Balarebe Abdullahi
- A gobe Jumu'a, 1 ga watan Disamba, Gwamna Abdullahi Sule zai gabatar da kasafin kudin 2024 ga majalisar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Mambobin majalisar dokokin jihar Nasarawa sun zaɓi sabon kakakin majalisar da kuma mataimakinsa ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba, 2023.
The Nation ta tattaro cewa yan majalisar sun zaɓi Ɗanladi Jatau mai wakiltar mazaɓar Kokona ta gabas a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin Nasarawa.
Jatau, mamban jam'iyyar APC mai mulki ya zama sabon shugaban majalisar ne ƙasa da awanni 48 bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tsige tsohon kakakin, Ibrahim Balarebe Abdullahi.
N27.5tr: Majalisar wakilan tarayya da Sanatoci sun fara tafka mahawar kan kudirin kasafin kuɗin 2024
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma mambobin sun zaɓi Mohammed Oyanki, mai wakiltar mazaɓar Doma ta kudu a inuwar jam'iyyar PDP a matsayin mataimakin shugaban majalisar dokokin.
Bayanai sun nuna hakan ba zai rasa nasaba da shirin Gwamna Abdullahi Sule na gabatar da kasafin kuɗin 2024 ga majalisar ranar Jumu'a.
Yadda kotu ta tsige kakakin majalisar Nasarawa
Idan baku manta a ranar Talata, Kotun daukaka kara mai zama a Abuja, a hukuncin da ta yanke, ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa.
Kafin kotu ta tsige shi, Abdullahi mamban jam’iyyar APC ne, wanda ya fara zuwa majalisar a shekarar 2015 kuma aka zabe shi a matsayin kakakin majalisar.
An sake zaben shi a matsayin mamba da kakakin majalisa a 2019 kuma ya sake samun nasara a 2023.
Ya kasance mamba mai wakiltar mazabar Umesha/Ugya ta karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Kotun daukaka kara ta ayyana Sa’ad Abdullahi Ibrahim na jam’iyyar PDP a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben mazabar Umaisha/Ugya a ranar 18 ga Maris 2023.
Shugaba Tinubu ya naɗa shugabar NIS
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da naɗin Wura-Ola Adepoju a matsayin kwanturola Janar ta hukumar NIS ta ƙasa.
Ƙafin wannan naɗi, Adepoju tana riƙe da matsayin mukaddashin shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS).
Asali: Legit.ng