Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama Kan Shari’ar Zaben Dan Majalisar PDP, Ta Bayyana Mai Nasara
- Kotun daukaka kara a jihar Legas ta raba gardama a shari'ar zaben Majalisar jihar Abia
- Kotun ta tabbatar da nasarar dan takarar PDP, Dennis Rowland Chinwendu a mazabar Isiala Ngwa
- Har ila yau, kotun ta yi watsi da dan takarar jam'iyyar LP saboda rashin gamsassun hujjoji
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Abia – Kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Legas ta raba gardama kan shari’ar zaben mazabar Isiala Ngwa ta Kudu da ke jihar Abia.
Kotun ta tabbatar da nasarar Dennis Rowland Chinwendu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris, Legit ta tattaro.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Chinwendu wanda jigo ne a jam’iyyar PDP shi ne shugaban kwamitin harkar noma a majalisar jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun har ila yau, ta yi fatali da karar dan takarar jam'iyyar LP, Dannie Ubani kan rashin gamsassun hujjoji.
Har ila yau, kotun ta bayyana cewa dan takarar LP ya gaza tabbatar da korafinsa na cewa zaben Chinwendu bai inganta ba.
Wane martani Chinwendu ya yi?
A martaninshi, Chinwendu ya ce wannan nasara ba ta shi kadai ba ne inda ya ce nasarar ta dukkan mazabar Isiala Ngwa ce.
Ya yi alkawarin ci gaba aikin alkairi da kuma kawo abubuwan ci gaba inda ya bukaci 'yan kungiyar Ebubedike su ci gaba da jajircewa da ayyukansu.
Wannan na nasara ta Chinwendu ta zo dai-dai da babban taron shekara da kungiyar Ebubedike ke gudanarwa.
Chinwendu shi ne shugaban kwamitin amintantattu na kungiyar (BOT) inda su ka hada da murnar nasarar Chinwendu yayin taron.
Da ya ke magana, Henry Orih, kwadinetan kungiyar ya godewa ubangiji kan wannan nasara da ya ba su.
Kotu ta yi hukunci kan dan Majalisa 1 a Plateau
A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben Majalisar jihar Plateau.
Kotun ta kwace kujerar dan takarar PDP, Cornelius Doeyok saboda rashin tsari a jam'iyyar.
Har ila yau, kotun ta tabbatar da nasasar dan takarar APC, Farfesa Bala Theodore Maiyaki a matsayin wanda ya lashe zaben.
Asali: Legit.ng