Ministan Jonathan Ya Shaidawa Kotu Yadda Aka ba Tsohon Gwamna N1.2bn a Lashe Zabe

Ministan Jonathan Ya Shaidawa Kotu Yadda Aka ba Tsohon Gwamna N1.2bn a Lashe Zabe

  • Musiliu Obanikoro ya bada shaida a kotun tarayya da ke garin Abuja a shari’ar da ake yi tsakanin EFCC da Mr. Ayodele Fayose
  • Tsohon karamin Ministan tsaron ya fadawa Alkali cewa Sambo Dasuki ya aiko masa kudi wanda aka kai wa tsohon gwamnan
  • PDP ta ci zaben Gwamnan Ekiti a 2014, hukumar EFCC na zargin Ayodele Fayose da satar N6.9bn a lokacin Dr. Goodluck Jonathan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Musiliu Obanikoro wanda ya rike karamin Ministan tsaro a Najeriya, ya bada shaida a shari’ar hukumar EFCC da Ayodele Fayose.

Hukumar EFCC ta na tuhumar Ayodele Fayose da hannu wajen karkatar da N6.9bn kafin da lokacin ya na gwamnan Ekiti a inuwar PDP.

Kara karanta wannan

Batun shari’ar zaben Kano ya yi girma, NNPP ta kai magana ECOWAS, EU da Amurka

GovAyoFayose, @MObanikoro
EFCC v Tsohon Minista da Tsohon Gwamna Ayo Fayose Hoto: @GovAyoFayose, @MObanikoro
Asali: Twitter

Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na Twitter, an koma kotun tarayya da ke Abuja domin cigaba da sauraron shari’arta da Fayose.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC: Musiliu Obanikoro ya tona Fayose

A ranar Laraba, Sanata Musiliu Obanikoro ya fadawa kotu cewa gazawa wani banki wajen aika kudin ya jawo su ka dauki tsabar kudi a hannu.

Musiliu Obanikoro ya shaidawa Mai shari’a Nnamdi Dimgba yadda su ka kinkimi N1.219bn, aka mikawa Ayodele Fayose lokacin ana shirin zabe.

EFCC ta na binciken kudin makamai

Da lauyan EFCC, Wahab Shittu, SAN ya bukaci karin haske kan inda kudin su ka fito, sai Obanikoro ya nuna masa daga ofishin NSA ne aka karbo su.

‘Dan siyasar ya ce Kanal Sambo Dasuki (retd) ya tuntube shi lokacin ya na Minista, ya ce an tura biliyoyin kudin zuwa kamfanin Sylvan Mcnamara Ltd.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya bankaɗo matsala kan yan ta'adda, ya buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa jihohi 6 a arewa

Amsar da Musiliu Obanikoro ya ba EFCC

"A lokacin ni ke kula da harkokin zaben. Kwanaki kafin zabe sai na ga kira daga gwamna Fayose, ya na tambaya ko ina da sako da zan ba shi daga ONSA.
Zan iya tunawa cewa kafin nan mun yi wasu taro da shirin zaben. Da Fayose ya kira, sai na fada masa zan kira shi daga baya, sai na tuntubi NSA a waya.
Bayan ya sake kira sai ya shaida mani an tura N2.2bn zuwa asusun Sylvan Mcnamara Ltd."

- Musliu Obanikoro

Kudin Boko Haram ko kudin PDP?

Tsohon Sanatan ya ce Dasuki kurum zai iya bayanin silar wadannan kudi, ya ce an ba kamfanin Sylvan Mcnamara kwangilar yaki da Boko Haram.

Ranar 27 ga watan Fubrairu za a cigaba da sauraron karar a kotun tarayyan na Abuja.

Yadda Fayose ya taimaki APC

Mun taba kawo rahoto inda aka ji Ayodele Fayose ya fadi dalilinsa na marawa Bola Tinubu baya kan PDP da ta tsaida Atiku Abubakar a zaben 2023.

Fayose ya ce bai harin zama Minista, a cewarsa duk wanda ya kai shekara 65, kamata ya yi ya kai wa Tinubu snayen yaran da zai ba mukami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng