Hukumar EFCC ta nemi Fayose ya maido da naira biliyan 1.3 kudin da ya handama

Hukumar EFCC ta nemi Fayose ya maido da naira biliyan 1.3 kudin da ya handama

Tsohon gwamnan jahar Ekiti, Ayodele Fayose ya amsa gayyatar hukumar EFCC a ranar Talata sakamakon karewar kariyar da yake da shi a matsayinsa na gwamna bayan wa’adin mulkinsa ya kare, inda ya sha tambayoyi da binciken kwakwaf.

Jaridar Punch ta ruwaito a yayin da aka shigar da Fayose dakin bincike, jami’an hukumar sun bukace shi daya rubuta duka abinda ya sani da kuma yadda ya kashe makudan kudade da suka kai naira biliyan daya da miliyan dari uku da suka ce ya karba daga ofishin Sambo Dasuki gabanin zaben jahar na 2014

KU KARANTA: Gwamna Fayemi ya nada wasu muhumman mukamai da zasu tafiyar da gwamnatinsa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani jami’in hukumar ya bayyana mata cewa hukuma ta bukaci gwamnan daya dawo da wadannan kudade domin haramtattu kudade ne da aka fitar dasu ba akan ka’ida ba, sai dai Fayose yayi tirjiya, inda yace bai amshi ko sisi daga Sambo Dasuki ba.

Hukumar EFCC ta nemi Fayose ya maido da naira biliyan 1.3 kudin daya handama
Isar Fayose ofishin EFCC
Asali: Facebook

“A gaskiya mun girmama Fayose tun bayan da ya kawo kansa ofishinmu, mun tambayeshi game da kudaden da Obanikoro ya kai masa, wanda ya amsosu dagaa wajen tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa Godluck Jonathan akan harkokin tsaro, kanal Sambi Dasuki.

“Mun nemi ya dawo da kudaden, amma yace bai amsh ko sisi daga hannun Obanikoro ba, a bayanin da yayi yace bai taba karbar ko sisi ba, duk da cewa muna da kwararan hujjoji game da wannan badakala, baya son ya bamu hadin kai bisa dukkan alama.” Inji shi.

Wannan kudi da hukumar EFCC ke tuhumar Fayose dasu na daga cikin adadin kudi naira biliyan hudu da miliyan dari bakwai da ake zargin Sambo Dasuki ya baiwa tsohon ministan kudi, Musliu Obanikoro a gabanin zaben gwamnan jahar Ekiti na shekarar 2014 wanda Fayose ya lashe.

Tun a shekarar 2015 da EFCC ta fara bin diddigin wannan badakala, ta yi ma akalla mutane 20 tambayoyi, daga cikinsu akwai tsohon minista Obanikoro, tsohon gwamnan jahar Osun Omisore, Ahmed Borodo direban jirgin saman daya dauki kudi daga Legas zuwa Ekiti, jami’in tsaron Obanikoro Laftanar Olumide Adewale, da hamidin Fayose Abiodun Agbele, sauran sun hada da yan canji da shuwagabannin bankuna.

A wani hannun kuma, lauyan Fayose, Mike Ozekhome ya bayyana cewa Fayose ba zai taba amsa laifin da bai yi ba, don kuwa tun tuni EFCC ta daskarar da asusun bankinsa, wanda a yanzu haka ya shigar da kara Kotu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng