Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Tsige Mataimakin Gwamnan APC, Ta Fadi Dalili

Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Tsige Mataimakin Gwamnan APC, Ta Fadi Dalili

  • Yayin da ake ci gaba da rikici kan tsige mataimakin gwamnan jihar Ondo, Majalisar jihar ta janye karar da ta shigar
  • Wannan na zuwa ne bayan ta shigar kara kotu inda ta ke kalubalantar hana ci gaba da shirin tsige mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa
  • Matakin bai rasa nasaba da shiga rigimar da Shugaba Bola Tinubu ya yi don kawo karshen rigimar a wannan makon

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Majalisar jihar Ondo ta janye karar da ta shigar kotun daukaka kara kan shirinta na tsige mataimakin gwamnan jihar.

Majalisar ta samu cikas a kotun Tarayya bayan ta hana ta ci gaba da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama kan shari'ar zaben dan Majalisar PDP, ta bayyana mai nasara

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar tsige gwamnan APC
Kotun ta raba gardama a shari'ar tsige Gwamna Akeredolu. Hoto: Rotimi A., Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke kan rikicin siyasar?

Kotun daukaka kara ta kuma kalubalanci kotun Tarayyar da ta ji korafin Lucky don dakile hana tsige shi a kujerar mataimakin gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalan kotun karkashin jagorancin Haruna Tsammani ta yi watsi da korafin bayan lauyan Majalisar, Remi Olatubora ya janye karar, cewar The Nation.

Olatubora yayin janye karar ya ce wadanda ke cikin shari'ar sun samu daidaito a siyasance kuma sun amince.

A ranar 26 ga watan Satumba ce kotun Tarayya ta hana Majalisar da kakakinta yunkurin tsige mataimakin gwamnan.

Wane mataki Majalisar ta dauka a baya kan rikicin?

Daga bisani, Majalisar da kakakinta sun daukaka kara kan matsalar a ranar 3 ga watan Oktoba kafin yanzu su janye karar bayan samun maslaha.

Daga cikin wadanda shari'ar ta shafa akwai gwamnan jihar Ondo da shugaban alkalan jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu: Kotun daukaka kara ta tsige mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar PDP a arewa

Sauran sun hada da kakain Majalisar jihar da ita kanta Majalisar da kuma sauran wadanda abin ya shafa.

Legit ta tattaro cewa a yau mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa shi ya jagoranci zaman Majalisar zartarwa a yau Alhamis 30 ga watan Nuwamba.

Lucky Aiyedatiwa zai yi murabus

A wani labarin, mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa zai mika takardar murabus daga mukaminsa.

Kakakin Majalisar jihar, Olamide Oladiji shi ya bayyana haka inda ya ce matakin ya biyo bayan saka baki da Shugaba Tinubu ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.