Zaben Kano: Yawan Kuri'u Ba Shi ne Kadai Alamar Nasara a Zabe Ba, Cewar Doguwa

Zaben Kano: Yawan Kuri'u Ba Shi ne Kadai Alamar Nasara a Zabe Ba, Cewar Doguwa

  • Dan majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa, ya magantu kan dambarwar siyasa da ke faruwa a jihar Kano
  • Doguwa, wanda ya kasance mamba na APC a majalisar wakilai ya bayyana cewa yawan kuri'u kadai ba shi ke sa a ci zabe ba sai an bi tsari da dokoki
  • Dan majalisar na APC ya ce abun da ke faruwa yanzu haka a Kano, abu ne da aka saba gani a yanayin siyasar jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa cin zabe ba wai a iya yawan kuri’un da aka kada ba ne kawai, a'a har da bin ka’idojin wasa.

Doguwa ya yi wannan furucin ne a ranar Laraba, 29 a Channels TV, yayin da yake martani kan takaddamar da ke kewaye da zaben 2023 a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Neman karbe kujerar Abba Gida-Gida a kotu zalunci ne kawai, Malamin Musulunci

Doguwa ya ce ba yawan kuri'u ke sa a ci zabe ba
Yawan Kuri'u Ba Shi ne Kadai Alamar Nasara a Zabe Ba, Cewar Doguwa Hoto: Hon Alhassan Ado Doguwa/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Bin tsari da dokoki ke sa a ci zabe a kasa irin Najeriya - Doguwa

Ya bayyana cewa doka da tsare-tsaren zabe a kasa kamar Najeriya da ake bin tsarin damokradiyya, kuma shiga takarar zabe bisa wadannan dokoki shine ke sa shi zama na gaskiya da adalci, Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dogyuwa ya ce:

"A ra'ayina idan ka tambayeni game da abun da ke gudana a Kano, abu ne da ya saba faruwa, Kano ta kasance mai ci gaba a kodayaushe, jiha ce mai fafutuka ta fuskar siyasa da akida.
“Idan aka zo batun irin wannan, rigima a kodayaushe takaddama na shigowa a lamarin siyasarmu kuma kowa yana da ra’ayinsa.
"Abun da mutanenmu suka gaza fahimta ko wasu daga cikin mutanenmu shine rashin fahimtar cewa, zabuka musamman a tsarin dimokradiyya irin wanda muke gudanarwa a Najeriya a kodayaushe ya shafi ka’idojin wasa ne, ba wai kawai na ci zabe ba ne.

Kara karanta wannan

Manyan Arewa: Take-taken Tinubu sun nuna bai damu da gyara tsaron Arewa ba

"Cin zabe na iya zama shiga takara da yin nasara a zabe karkashin tsari da dokokin da aka shimfida kamar yadda dokar zabe ta tanada da kuma kundintsarin mulkin Najeriya. Yana daga cikin abun da ya zama dole mu bi don yin nasara a zabe na gaskiya da adalci.
“Zabe na gaskiya ba wai kawai kirga kuri’u kadai ba ne ko da kuwa an kirga kuri’u duk da haka akwai wasu kuri’u da aka ce ba sa bisa ka’ida.
"Don haka dole ne ku yarda da cewa eh abin da ake samu a cikin irin namu siyasar da dimokradiyya ba wai a Najeriya kadai ba shine bin ka'idojin wasan."

A zantawarsa da jaridar Legit Hausa, wani dan APC mai suna Mallam Aliyu ya jaddada wannan ikirari na Doguwa inda ya ce:

“Wannan batu ne da ya shafi doka, ko ka ci zaɓe a akwatu matuƙar ka saɓa wasu dokoki da ƙa'idojin da aka tanada to fa ba kai ka ci zaɓe ba.

Kara karanta wannan

Kaico: Shekaru biyar da ritaya, sufetan 'yan sanda ya koma barace-barace a titi

“Idan kika duba abinda ya faru a Filafo, PDP ta samu mafi rinjayen kuri'u ranar zaɓe amma tun farko sun saba wa umarnin kotu, yanzu kusan duk an kwace kujerun yan majalisu.
“To a Ƙano ma kusan haka ne, NNPP da ɗan takararta gwamna mai ci sun saɓa doka kuma kotu ta gano hakan, don haka maganar Doguwa gaskiya ce.
“Mu a APC muna fatan mu karbi Kano sabida tana da matuƙar muhimmanci idan kana son cin zabe a Najeriya.”

Doguwa ya kwancewa NNPP zani

A wani labarin, mun kawo a baya cewa tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa ya yi ikirarin cewa jam'iyyar NNPP ta tafka magudi a zaben jihar na 2023.

Ado Doguwa wanda dan majalisa ne yanzu mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa daga jihar Kano, ya ce NNPP ta yi amfani da kuri'un bogi a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng