Rikici Ya Sake Barkewa Tun Bayan Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan APC, PDP Ta Shiga Lahaula

Rikici Ya Sake Barkewa Tun Bayan Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan APC, PDP Ta Shiga Lahaula

  • Rikici ya sake bullowa tun bayan yanke hukuncin shari’ar zaben jihar Nasarawa da Gwamna Sule na jam’iyyar APC ya yi nasara
  • A jiya rundunar sojin kasar sun zargi magoya bayan jam’iyyar PDP da kai musu hari yayin da su ke zanga-zanga a Lafia
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin Lafia, Aminu Abdullahi wanda dan jam'iyyar PDP ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa – Jam’iyyar APC a jihar Nasarawa ta caccaki jam’iyyar mai adawa ta PDP kan zanga-zanga saboda hukuncin kotu.

APC ta zargi PDP ta gudanar da zanga-zangar don ta da zaune tsaye a jihar tare da kawo rudani don biyan bukatarta, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rikicin shari'ar Kano: An kai karar Gwamna Yusuf Majalisar Dinkin Duniya, bayani ya fito

Rikici na kara tsami tsakanin APC, PDP tun bayan yanke hukuncin shari'ar zabe
Jam'iyyar PDP na ci gaba da zanga-zanga kan hukuncin zaben jihar Nasarawa. Hoto: D. Ombugado, S. Abdullahi.
Asali: Twitter

Mene ya jawo rikici tsakanin APC, PDP?

Wannan na zuwa ne yayin da PDP ke kalubalantar hukuncin kotun da ta bai wa Gwamna Abdullahi Sule nasara a zaben, cewar Independent.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar ba ta aminta da hukuncin ba wanda ya kori karar dan takarar jam’iyyar PDP, David Ombugado a jihar.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Aliyu Bello ya ce PDP a suna ne kawai ta ke dimukradiyya amma dukkan abubuwanta ya sabawa doka.

Aliyu ya bayyana haka ne a jiya Laraba 29 ga watan Nuwamba yayin ganawa da manema labarai.

Mene martanin APC kan rikidewar PDP?

Shugaban jam’iyyar ya ce PDP ta kuma tara mata inda su ke zanga-zanga tsirara a kan tituna da kuma sakatariyar jam’iyyar.

Ya ce:

“An biya wadannan mata wadanda su ka fito tsirara su na zanga-zanga, wannan abin ya sabawa al’ada.

Kara karanta wannan

APC ta nuna yatsa kan wanda take zargi da kai mummunan farmaki gidan kwamishinan zabe a Kogi

“Dukkan shaidanun PDP yanzu su na ta ingiza su kuma sun yaudare su don mu zamu sake nasara a kotun koli.
“Ya tabbata mu zamu sake yin nasara ganin yadda hujjoji ke aiki a kotunan zabe tun daga kotun zabe har na daukaka kara.”

Kokarin jin martani daga bangaren jam’iyyar PDP ya ci tura har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin birnin Lafia, Aminu Abdullahi wanda dan jam'iyyar PDP ne.

Aminu ya ce dukkan wannan matsalar ta faru ne saboda rashin adalci da aka yi a hukuncin kotun.

Ya ce:

"Idan har za a yi rashin adalci a zabe ko hukuncin kotu to komai zai iya faruwa musamman rashin zaman lafiya da ya haddasa kai hari kan sojoji."

Masu zanga-zanga sun kai hari kan sojoji

A wani labarin, Rundunar sojin Najeriya sun yi Allah wadai da farmaki da masu zanga-zanga su ka kai musu a jihar Nasarawa.

Sojojin sun zargin ‘yan jam’iyyar PDP da kai musu farmaki yayin da su ke zanga-zanga kan hukuncin kotun daukaka kara a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.