Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Ta Zabi Sabon Kakakin Majalisa da Mataimakinsa
- Shugabanci ya sauya hannu a majalisar dokokin jihar Bauchi bayan ƴan majalisar sun zaɓi sabon kakakin majalisa da mataimakinsa
- Ƴan majalisar sun zaɓi Babayo Muhammad mai wakiltar mazaɓar Hardawa a matsayin sabon kakakin majalisar bayan kotu ta soke zaɓen tsohon kakakin
- Ahmad Abdullahi mai wakiltar mazaɓar Dass ya zama sabon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar ta Bauchi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Ƴan majalisar dokokin jihar Bauchi sun zaɓi sabon kakakin majalisar, biyo bayan yanke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na soke zaɓen kakakin majalisar a ranar Laraba da ta gabata.
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta soke zaɓen Abubakar Sulaiman saboda a cewarta yana cike da kura-kurai inda ta bayar da umarnin a sake zaɓe a rumfuna 10 na mazaɓar Ningi.
Su wane ne aka zaɓa?
Leadership ta ce ƴan majalisar sun zaɓi ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Hardawa, Babayo Muhammad a matsayin sabon kakakin majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, ƴan majalisar sun kuma zaɓi ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Dass, Ahmad Abdullahi, a matsayin mataimakin kakakin majalisar, rahoton The Punch ya tabbatar.
Kotun daukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, a wani hukunci da ta yanke, ta soke zaɓen mataimakin kakakin majalisar, Jamilu Umarau Dahiru, mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya.
Mai magana da yawun majalisar, Musa Nakwada, wanda ya tabbatar da zaɓen sabbin shugabannin majalisar, ya ce matakin da ƴan majalisar suka dauka ya zama dole ne domin cike gurbin da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ya jawo.
Za a sake gudanar da zaɓe a wasu rumfunan zaɓe na mazabun tsohon kakakin majalisar da mataimakinsa domin tantance waɗanda suka lashe lashe zaɓen.
Rigima Ta Ɓalle a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu ɓarkewar rikicin shugabanci a majalisar dokokin jihar Bauchi, biyo bayan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na soke zaɓen kakakin majalisar da mataimakinsa.
bayan tsige shugaban majalisar dokokin da mataimakinsa, kwatsam sai rikici ya ɓalle tsakanin mambobin majalisar kan shugabanci.
Asali: Legit.ng