PDP Ta Shiga Tangal-Tangal Yayin da Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai Kan Rikicin Wike da Fubara

PDP Ta Shiga Tangal-Tangal Yayin da Sabuwar Rigima Ta Kunno Kai Kan Rikicin Wike da Fubara

  • An sake gudanar da zanga-zanga a sakatariyar PDP ta ƙasa kan kiran da aka yi na korar shugaban jam'iyyar na ƙasa Umar Damagum
  • Wata ƙungiya a jam’iyyar, Concerned PDP League (CPDPL), ta ce Damagum ya yi wa jam’iyyar aiki, don haka a bar shi ya cigaba da shugabancin PDP
  • Jagoran zanga-zangar, Daboikiabo Warmate, ya bayyana cewa Damagum ne ya fara tsoma baki a rikicin siyasar da ya ɓarke tsakanin Gwamna Sim Fubara da Nyesom Wike

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta sake faɗawa cikin wani rikici yayin da wasu ƴaƴan jam’iyyar suka gudanar da zanga-zanga a sakatariyarta ta ƙasa domin nuna adawa da kiran da aka yi na a tsige shugaban jam’iyyar na ƙasa Umar Damagum.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Babban malamin addini ya yi magana kan yiwuwar sasanta wa tsakanin Wike da Fubara

A ƙarƙashin inuwar Concered PDP League (CPDPL), shugaban ƙungiyar, Kwamared Daboikiabo Z. Warmate, ya lissafo nasarorin da muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa ya samu.

An goyi bayan shugaban PDP na kasa
Shugaban PDP na kasa ya taka muhimmiyar rawa a rikicin Wike da Fubara Hoto: Nyesom Wike, Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa Damagum ne ya fara tsoma baki a rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Warmate, Damagum ya tattauna da Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, kan rikicin sannan ya tattauna da Siminalayi Fubara, kafin Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani.

Dalilin da yasa masu zanga-zanga suka mamaye sakatariyar PDP ta ƙasa

Ya ce yana da kyau jam’iyyar ta cigaba da zama a dunƙule domin hana Najeriya rikiɗewa zuwa jam’iyya daya, inda ya goyi bayan zargin da Atiku Abubakar ya yi na cewa jam'iyyar APC na shirin mayar da Najeriya ƙasa mai jam'iyya daya.

Da yake jawabi ga manema labarai a filin zanga-zangar, Warmate ya ce:

Kara karanta wannan

Shugaban jam'iyyar PDP ya yi murabus bayan Bola Tinubu ya naɗa shi a babban muƙami

"A bisa binciken da muka yi, zan iya gaya muku, shugaban jam’iyyar na ƙasa, Umar Damagum ne ya fara tuntuɓar ɓangarorin da ke rikici da juna, wato Wike da Sim Fubara, amma saboda batun jam’iyya ne, kafafen yaɗa labarai ba su bayar da rahoton hakan ba."

A cikin wani faifan bidiyo da Legit.ng ta gani, masu zanga-zangar sun yi kaca-kaca da kiran korar Damagum, inda suka bayyana cewa kamata ya yi a yaba wa muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa kan yadda ya yi ƙoƙarin haɗa kan jam'iyyar, inda suka ƙara da cewa dole ne kowa ya hada kai domin kafa babbar adawa.

Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Rikicin Wike da Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya yi magana kan rikicin Wike da Gwamna Fubara na Rivers.

Babbban malamin addinin ya bayyana cewa zai yi wuya a sasanta ƴan siyasar biyu saboda Wike ba zai yafe wa Gwamna Fubara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng