Sabuwar Rigima Ta Ɓalle a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Bayan Hukuncin Kotun Ɗaukaka Kara
- Hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ya haddasa sabon rikicin shugabnci a majalisar dokokin jihar Bauchi ranar Talata
- Kotun ta tsige kakakin majalisar da mataimakinsa, ta umarci INEC ta shirya sabon zabe a wasu rumfunan mazaɓu biyu
- Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Musa Wakili Nakwada, ya ce zasu bi matakan da doka ta tanada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka rikicin shugabanci ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Bauchi bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.
Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ɗaukaka ƙara, ranar Jumu'a, ta tsige shugaban majalisar dokokin Bauchi, Abubakar Y Suleiman, kana ta bada umarnin canja zaɓe a mazaɓarsa, Ningi ta tsakiya.
Ranar Talata kuma kotun mai zama a Abuja ta tuge mataimakin shugaban majalisar, Jamilu Umaru Dahiru, nan ma ta umarci sauya zaɓe a Bauchi ta tsakiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abinda ya biyo bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara
Leadership ta ce bayan tsige shugaban majalisar dokokin da mataimakinsa, kwatsam sai rikici ya ɓalle tsakanin mambobin majalisar kan shugabanci.
Yayin da aka tuntuɓe shi, shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dokokin jihar Bauchi, Honorabul Musa Wakili Nakwada, ya ce zasu bi matakan da suka dace bisa tanadin doka.
Ɗan majalisar ya ce:
"A matsayinmu na mambobin majalisa ba za mu yi komai ba amma za mu bi ka’ida da kuma hakikanin abin da ya kamata a yi kamar yadda doka da kundin tsarin mulki suka tanada."
Shin yan majalisar zasu zabi sabbin shugabanni?
Da aka tambaye shi ko za su zabi sabon kakakin majalisa da mataimakinsa, Nakwada ya ce:
"Na faɗa muku zamu bi matakai da ƙa'idojin da suka dace, idan doka ta amince mu yi hakan zamu yi, idan kuma doka ta hana mu yi hakan to ba zamu yi ba."
"Zamu bi umarnin doka da duk abin da kundin tsarin mulki ya tanada, zamu tabbata mun yi abinda yake daidai."
Shugaba Tinubu Ya Aike da Wasiƙa Ga Majalisar Dattawa
A wani rahoton na daban Shugaban ƙasa Tinubu ya sanar da shirinsa na gabatar da kasafin kuɗin idan Allah ya kaimu ranar Laraba (gobe), 29 ga watan Nuwamba, 2023.
Wannan ne karo na farko da Bola Tinubu zai gabatar kudirin kasafin kuɗin shekara tun bayan hawa gadon mulki a watan Mayu.
Asali: Legit.ng