Jam’iyyar PDP Ta Garzaya Kotun Koli Don Kalubalantar Shari'ar Gwamnan APC, Ta Koka da Zaluncin Kotu
- Bayan yanke hukuncin kotun daukaka kara, jam'iyyar PDP za ta daukaka zuwa kotun koli don neman hakkinta
- Jam'iyyar na kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ta yi kan zaben Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas
- Wannan na zuwa ne bayan kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaben
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Legas ta garzaya kotun koli don kalubalantar nasarar Gwamna Sanwo-Olu.
Jam'iyyar ta ce an yi kuskure wurin tabbatar da nasarar Sanwo-Olu a matsayin gwamnan jihar, cewar TheCable
Mene PDP ke cewa kan hukuncin?
Sakataren yada labarai na jam'iyyar a jihar Legas, Hakeem Amode shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakeem yayin ganawar a yau Litinin 27 ga watan Nuwamba ya ce kotun daukaka kara ta yi rashin adalci a hukuncin.
A watan Maris, Hukumar INEC ta ayyana Gwamna Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna jihar, Pulse ta tattaro.
Sanwo-Olu ya samu kuri'u 762,134 yayin da dan takarar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour ya samu kuri'u 312,329.
Yayin hirar, Amode ya ce sun daukaka kara zuwa kotun koli a kwanakin nan inda ya ce su na fatan samun adalci a can.
Martanin PDP kan shari'ar zaben Legas
Ya ce:
"Mu na kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara kuma za mu daukaka kara a 'yan kwanakin nan zuwa kotun koli.
"Ganin yadda wasu hukunce-hukuncen kotun daukaka kara ta kasance, akwai matsaloli da dama a cikin hukuncin.
"A matsayin jam'iyya, mun tabbatar cewa ba a yi hukuncin adalci ba a karar da mu ke yi na zaben watan Maris."
Amode ya kara da cewa su na da tabbacin samun hukuncin adalci da kuma gyara kura-kuran baya.
Kotu ta yi hukunci a shari'ar Legas
A wani labarin, kotun daukaka kara ta raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Legas.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng