Rikicin Rivers: Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Sasanta Wa Tsakanin Wike da Fubara

Rikicin Rivers: Babban Malamin Addini Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Sasanta Wa Tsakanin Wike da Fubara

  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya buƙaci gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da ya shirya fuskantar ƙarin matsaloli
  • Jihar Rivers dai ta fada cikin rikicin siyasa tun a ƙarshen watan Oktoba bayan yunkurin tsige Gwamna Fubara da wasu ƴan majalisar dokokin jihar suka yi
  • Rahotanni sun bayyana cewa ƴan majalisar da suka so tsige Fubara sun yi aiki ne bisa umarnin wanda Gwamna Fubara ya gada, Nyesom Wike

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi magana kan rashin jituwar da ke tsakanin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Babban faston ya bayyana cewa ba lallai ba ne rikicin na manyan ƴan siyasar jam'iyyar PDP a jihar ta Rivers ya zo ƙarshe nan kusa ba kamar yadda wasu ke zato.

Kara karanta wannan

Juyin mulki a kasar Saliyo? Abin da muka sani yayin da gwamnati ta sanya dokar hana fita

Ayodele ya yi magana kan rikicin Wike da Fubara
Primate Ayodele ya ce rikicin Wike da Gwamna Fubara ba zai kare nan kusa ba Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Primate Ayodele ya ce hakan ya faru ne saboda zai yi wuya Wike ya yafe wa gwamnan Rivers na yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Matsalar Fubara yanzu ta fara" - Ayodele

Malamin addinin ya ce yana hango ƙarin takaici a gaban Gwamna Fubara.

A cikin wani faifan bidiyo da ya sanya a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Lahadi, 26 ga watan Nuwamba, ya bayyana cewa:

"Gwamnan jihar Ribas da Wike. Ya kamata gwamnan jihar Ribas ya shirya tsaf domin yaki. Wanda ya gabace shi zai ba shi takaici, ba zai yafe masa ba, zai hana shi abubuwa da yawa, kuma zai yi amfani da jam’iyyarsa a kansa."
Domin haka gwamnan yanzu ya fara da matsalarsa. Maganar gaskiya rikici ne mai girma wanda zai fuskanta. Sannan babu wani abin da gwamnan zai yi da za a yaba masa."

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Gwamna Fubara Ya Tsokano Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya kare tsatsonsa na ƙabilar Ijaw inda ya ce ba ya tsoron kowa.

Kalaman gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicinsa da magabacinsa kuma ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike yake ƙara ƙamari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng