Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci a Shari'ar Kakakin Majalisa a Kaduna, Ta Umarci Sake Zabe
- Kitun daukaka kara ta sake rusa zaben kakakin Majalisar jihar Kaduna wanda ya kasance dan jam'iyyar APC
- Kotun, har ila yau, ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar PDP, Solomon Nuhu a matsayin wanda ya lashe zaben a mazabar Makera
- Kotun ta umarci sake zabe a wasu mazabu biyar da ke mazabar Makera a cikin jihar saboda samun matsaloli a zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben kakakin Majalisar jihar Kaduna.
Kotun ta kwace kujerar kakakin Majalisar Yusuf Dahiru Liman na jam'iyyar APC inda ta umarci sake zabe a mazabu biyar, cewar Tribune.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben, Solomon Nuhu ya kalubalanci zaben Liman da ke wakiltar mazabar Makera a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nuhu ya ce akwai kura-kurai da aka tafka yayin zaben inda ya tabbatar da cewa shi ya lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.
A zaben da aka gudanar, Liman na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 17,740 yayin da takwaransa na jam'iyyar PDP, Nuhu ya samu kuri'u 17,088.
Wasu mazabu za a sake zabe?
Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, O. Adejumo a ranar Juma'a 24 ga watan Nuwamba ta kori karar da dan jam'iyyar APC ya shigar.
Kotun ta umarci sake zabe a wasu mazabu da su ka hada da Unguwar Barnawa mazaba ta 005 da 009 sai Kakuri a mazabar 006.
Sauran sun hada da Unguwar Television a mazaba ta 002 sai kuma Kakauri Hausa a mazaba 045, cewar Channels TV
Kotu ta yi hukunci a shari'ar gwamnan Kaduna
A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kaduna da aka gudanar a watan Maris.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
Har ila yau, ta yi watsi da korafin dan takarar jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan saboda rashin gamsassun hujjoji.
Asali: Legit.ng