Rashin Fahimtar Turanci Ke Sa Cewa Akwai Kuskure a CTC, Kperogi Ya Zargi Alakai Kan Hukuncin Kano
- Yayin da ake ci gaba da tofa albarkacin baki kan fitar da takardun CTC, Farfesa Farouk Kperogi ya yi martani kan matsalar
- Kperogi ya ce wadanda ba sa fahimtar Turanci ne kawai za su kira hakan da kuskure a ciki daman haka hukuncin ta ke
- Farfesan ya ce ya tabbata alkalan kotun sun yi hukunci ne ba tare da duba hukuncin karamar kotun ba a baya
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Farfesa Farouk Kperogi ya yi martani kan fitar da takardun CTC da kotun daukaka kara ta yi a Kano.
Kperogi ya ce babu wata maganar kuskure a cikin takardun CTC da kotun ta fitar da ya jawo cece-kuce, Legit ta tattaro.
Mene Kperogi ke cewa kan hukuncin Kano?
Farfesan ya ce ya tabbata alkalan kotun sun yi hukunci ne ba tare da duba hukuncin karamar kotun ba a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce daga bisani an samu wasu abubuwa da su ka sha bam-ban da hukuncin wanda hakan ya tilasta su sake rubuta hukuncin nasu.
Ya ce:
“A yayin sake rubuta hukuncin nasu, sun yi fatali da hukuncin karamar kotun a baya wanda hakan ya jawo cece-kuce."
Kperogi ya bayyana ma'anar kuskure
Ya kara da cewa:
“Wannan kuskure da su ke magana ba komai ba ne illa burbudin kura-kurai a baya, wadanda ba sa fahimtar Turanci ne za su kira hakan kuskure.”
Kperogi ya ce ta yaya za a ce wai takardun CTC an yi kuskure a ciki, ba zai yiwu ace dukkan abin da aka rubuta kuskure ba ne.
Ya ce abin da ake kira da kuskure shi ne rubuta wani abu ko harafi wanda hakan ba zai sauya komai a shari’ar ba.
‘Yan sanda sun gargadi APC, NNPP kan zanga-zanga
A wani labarin, rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta gargadi magoyan bayan jam’iyyun APC, NNPP kan gudanar da zanga-zanga a jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin yin zanga-zanga bayan fitar da takardun CTC da su ka jawo cece-kuce.
Asali: Legit.ng