APC Ta Mamaye Majalisar Jihar PDP Bayan Kotu Ta Kwace Dukkan Kujeru 16, an Shiga Yanayi
- Bayan kotun daukaka kara ta sake kwace kujerar dan Majalisa a jihar Plateau, yanzu PDP ta rasa kujerunta 16
- Wannan na zuwa ne bayan kotun ta kwace kujerar dan takarar PDP, Nannim Langyi a mazabar Langtang ta Arewa
- Kotun har ila yau, ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar APC, Nimchak Nansak a matsayin wanda ya lashe zabe
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta sake kwace kujerar dan majalisar jihar Plateau.
Kotun ta tabbatar da nasarar Nimchak Nansak na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Langtang ta Arewa.
Wane hukunci kotun ta yanke?
A watan Maris ne hukumar zabe ta ayyana Nannim Langyi na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Majalisar jihar, TheCable ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin hukuncin, alkalan guda uku sun yi watsi da hukuncin karamar kotun inda su ka ce bai kamata Langyi ya tsaya takara ba.
Kotun ta kara da cewa jam'iyyar ta ruguza tsarin ta tun shekarar 2020 don haka ba ta da hurumin tsayar da 'yan takara.
Alkalin kotun, Abang Okon ya ce dukkan kuri'un da dan takarar PDP ya zamu a banza ne.
Kujeru nawa APC ta mamaye?
Alkalin ya ce:
"Nimchak Nansak na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u mafi yawa shi ne ya lashe zaben Majalisar jihar.
"Nansak shi ne wanda ya lashe zabe a mazabar Langtang ta Arewa da aka gudanar a watan Maris."
Bayan yanke hukuncin, a yanzu PDP ta rasa dukkan kujerun majalisar 16 yayin da APC ke da kujeru 22, Legit ta tattaro.
Kotun ta kwace kujerar Mutfwang
A wani labarin, kotun daukaka kara ta kwace kujerar Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau wanda ke jami'yyar PDP.
Kotun ta kuma tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar APC, Nentawe Goshwe a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Har ila yau, kotun ta umarci hukumar zabe da ta yi gaggawar mika satifiket na cin zabe ga Nentawe Goshwe na APC.
Asali: Legit.ng