Abin Kunya Yayin da Dan Takarar Gwamna a Jam’iyyar NNPP Ya Shiga Hannu Kan Zargin Damfarar N607m

Abin Kunya Yayin da Dan Takarar Gwamna a Jam’iyyar NNPP Ya Shiga Hannu Kan Zargin Damfarar N607m

  • Wani dan siyasa ya shiga hannun ‘yan sanda bayan zargin damfarar wani kamfanin Kirifto da ake kira Patricia
  • Wanda ake zargin, Wilfred Bonse ya yi takarar gwamna a jam’iyyar NNPP a jihar Kuros Riba a wannan shekara ta 2023
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Muyiwa Adejobi ya tabbatar da kama dan siyasar a jiya Juma’a 24 ga watan Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kuros Riba – Rundunar ‘yan sanda ta cafke wani dan takarar gwamna a jam’iyyar NNPP kan zargin damfara.

Wanda ake zargin mai suna Wilfred Bonse ya tsaya takarar gwamna a zaben gwamnan jihar Kuros Riba a 2023, TheCable ta tattaro.

'Yan sanda sun cafke dan takarar gwamnan NNPP kan damfara
Dan takarar gwamna a NNPP ya shiga hannun 'yan sanda. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Mene ake zargin dan takarar NNPP da shi?

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Atoni Janar na Kano Dederi ya shiga matsala, an nemi a hukunta shi

Ana zargin Bonse da damfara da kuma ta da hankula ga wani kamfanin Kirifto da ake kira Patricia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Muyiwa Adejobi ya tabbatar da kama dan siyasar a jiya Juma’a 24 ga watan Nuwamba.

Muyiwa ya ce zargin Bonse da karkatar da naira miliyan 50 daga naira miliyan 607 na kamfanin da su ka damfara, Nairametrics ta tattaro.

Kakakin rundunar ya kara da cewa Bonse ya karkatar da kudaden ne ta bankinsa ta hanyar amfani da asusun Kirifto.

Wadannan kudade na daga cikin naira biliyan biyu da kamfanin Patricia ya yi asara saboda damfara a watan Mayun 2023.

Martanin 'yan sanda kan dan takarar NNPP

Muyiwa ya kara da cewa jami’ansu sun yi kwakkwaran bincike inda su ka samu bayanai masu muhimmanci bayan rahoton kamfanin a hukumar.

A watan Faburairu, ana zargin Bonse da hada baki da wasu ‘yan damfara ta yanar gizo inda su ka damfari kamfanin naira miliyan 40.

Kara karanta wannan

PDP ta kara shiga matsala yayin da kotun daukaka kara ta tsige yan majalisa 11 a jihar Filato

Shugaban kamfanin Patricia, Hanu Agbodje ya ce dan siyasar ya dade ya na damfarar kamfanin inda ya sace naira miliyan 607.

NNPP ta amince da kudurin Atiku na ‘Maja’

A wani labarin, jam’iyyar NNPP ta amince da bukatar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na hadin kai.

Atiku ya nemi goyon bayan jam’iyyun adawa a kasar don kwace mulki a hannun jam’iyyar APC mai mulki a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.