Wasu Manyan Jiga-Jigan NNPP Sun Shiga Sabuwar Matsala Bayan Hukuncin Tsige Abba Gida-Gida

Wasu Manyan Jiga-Jigan NNPP Sun Shiga Sabuwar Matsala Bayan Hukuncin Tsige Abba Gida-Gida

  • Jam'iyyar NNPP ta bankaɗo wani rahoto na barazanar da ake yi wa jiga-jiganta da nufin ganin bayansu
  • A wasiƙar da ta aike ga IGP, NNPP ta ce wasu da ake wa laƙabi da yan bindigan da ba'a sani ba na shirin kai hari sakateriyar jam'iyya
  • Ta bukaci sufetan yan sanda ya ɗauki matakin kare rayuka da dukiyoyin shugabannin NNPP kuma ya gudanar da bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - New Nigeria People’s Party (NNPP) ta yi zargin cewa wasu mutane da suka lulluɓe da sunan yan bindigan da ba'a sani ba suna yi wa mambobinta barazana.

Jam'iyyar NNPP ta ce ana mata barazana.
Hukuncin Kano: "Mambobin mu na fuskantar babbar barazana" NNPP ga IGP Hoto: NNPP
Asali: Twitter

Jam'iyyar mai alamar kwandon kayan marmari ta yi zargin cewa yan bindiga sun yi barazanar kai hari babbar sakatariyar NNPP ta ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

A wata wasiƙa da jam'iyyar ta tura zuwa ofishin Sufetan yan sanda na ƙasa (IGP) ta ce mutanen sun yi barazana raba wasu kusoshin NNPP da duniya, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasiƙar mai taken, "barazana ga rayuwar wasu shugabannin NNPP: muna buƙatar a ɗauki matakin kare rayuka da dukiyoyi," na ɗauke da sa hannun shugaban NNPP, Abba Kawu Alli.

NNPP ta buƙaci IGP ya ɗauki mataki

Jam'iyyar ta buƙacin IGP da ya ɗauki matakan kare sakateriyar NNPP kana ta yi kira da gudanar da bincike don gano masu hannu a lamarin.

A rahoton Daily Post, wani sashin wasiƙar ya ce:

"Muna amfani da wannan kafa wajen sanar da ofishinka rahotannin da muka samu na barazana ga rayuka da dukiyoyin wasu shugabannin jam'iyyarmu, New Nigeria People's Party, (NNPP)."
“Bisa bayanan da muka samu, akwai wani makirci da wasu da suka kira kansu da ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba’ na kai farmaki sakatariyar NNPP ta kasa."

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro sun cika ko ina, NNPP da APC sun hakura da zanga zanga a Kano

"Haka nan kuma a lokaci guda sun shafa wa wasu shugabannin jam’iyyar fenti da nufin raba su da duniya. Muna kira a yi bincike kuma a samar da tsaro a kewayen sakateriyar mu."

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan kotun ɗaukaka kara ta tsige Abba Kabir Yusuf na jihar Kano kuma kwafin hukuncin ya zo da ruɗani.

Jam'iyyar APC ta rantsar da kwamitin rikon kwarya na jihar Ribas

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC karkashin Abdullahi Ganduje ta rantsar da sabon kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar reshen jihar Ribas

Ganduje ya ce wannan kwamitin zai maida hankali wajen jawo mambobin APC da suka sauya sheƙa su dawo gida kuma zai shirya taruka

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262