Shugaba Tinubu Ya Yi Sabbin Muhimman Naɗe-Naɗe Biyu a Hukumar NCS Ta Kasa
- Bola Ahmed Tinubu ya naɗa karin mambobin majalisar gudanarwa a hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) ranar Jumu'a
- Waɗanda shugaban ƙasar ya naɗa zasu wakilci kamfanoni masu zaman kansu na tsawon zango ɗaya watau shekaru huɗu
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya faɗi sunayen mutanen biyu da suka haɗa da, Aba Ibrahim da Muda Yusuf
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin mutum biyu a matsayin mambobin majalisar gudanarwa ta hukumar kwastam ta ƙasa (NCS).
Mutanen biyu da shugaban kasa ya naɗa zasu shafe tsawon zango ɗaya na shekaru huɗu a matsayin wakilan ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu a NCS.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen mutanen da Tinubu ya naɗa
Ya bayyana sunayen mutanen biyu da shugaba Tinubu ya naɗa a majalisar gudanarwan NCS wanda suka hada da, Dakta Aba Ibrahim da Dakta Muda Yusuf.
Gidan talabijin na kasa NTA ya tattaro sanarwan na cewa:
"Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa sabbin waɗanda aka naɗa fatan alheri a aikin da suka tasa a gaba kuma yana sa ran jin ra'ayoyi da hangen kamfanoni masu zaman kansu."
"Musamman a abin da ya shafi manufofin sabunta fatan yan ƙasa da kuma jawo hankalin masu zuba hannu jari a ɓangarori daban-daban na tattalin arziƙi, yayin da ake kokarin kawo sauyi a hukumar kwastam."
Shugaba Tinubu ya naɗa manyan sakatarori 10
Wannan naɗi na zuwa ne jim kaɗan bayan shugaban ƙasa Tinubu ya amince da naɗin sabbin manyan sakatarori 10 a ma'aikatar gwamnatin tarayya.
Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa hakan ya biyo bayan kammaƙa zaɓo mutanen da ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa ya yi.
Yan majalisa 27 sun juya wa gwamna baya
Kuna da labarin Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa mambobi 27 daga cikin 31 na majalisar dokokin jihar Ribas ba su tare da Gwamna Siminalayi Fubara
Mista Wike, ministan birnin tarayya Abuja ya bayyana haka ne a wata hira ranar Jumu'a kan danbarwar siyasar jihar Ribas
Asali: Legit.ng