Wike: Yadda Gwamnan Ribas Ya Tura a Kona Majalisar Dokoki Domin Hana a Tsige Shi

Wike: Yadda Gwamnan Ribas Ya Tura a Kona Majalisar Dokoki Domin Hana a Tsige Shi

  • A kaddara Nyesom Wike yana da hannu wajen yunkurin tsige Gwamna Simi Fubara a majalisar dokokin Ribas
  • Minstan na Abuja ya zargi Gwamnan Ribas da sakin layin da suka dauko, ya ce gwamnati ta kama wani layin dabam
  • A cewar Wike, Fubara ne ya tura mutane su kona majalisar dokoki da ya fuskanci ana yunkurin tunbuke shi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja – Mr. Nyesome Wike ya zargi magajinsa watau Mai girma Sim Fubara da hannu a wajen kona majalisar dokokin jihar Ribas.

A wata hira da AIT ta yi da Ministan harkokin birnin tarayyan na Abuja, ya yi karin haske game da rigimarsa da Gwamna Sim Fubara.

Gwamna Simi Fubara
Simi Fubara ya na fada da Nyesom Wike Hoto:@Topboychris
Asali: Twitter

Rikicin siyasar Nyesom Wike v Fubara

Kara karanta wannan

Wike ya magantu kan yiwuwar karawa da Tinubu a zaben 2027

An yi ta fama da rikicin siyasa kwanakin baya, hakan ne aka ji ya yi sanadiyyar tsige Edison Ehie daga kujerarsa a majalisar dokoki..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga baya Hon. Ehie da wasu ‘yan majalisan dokoki da ke tare da Fubara, sun maida martani kan tunbuke shugaban masu rinjayen.

Daily Post ta rahoto Ministan ya na bayanin abin da ya jawo sabaninsa da magajinsa.

Zargin da Wike ya yi wa Gwamna Fubara

"A lokacin da su ke shirin tsige ka, ka kira ni ka fada mani cewa,’’Yallabai, su na so su tsige ni’
Wannan ne ya jawo ka tura mutane su kona zauren majalisa? Tsige (gwamna) aikin rana guda ne?
Aikin tunbuke (gwamna) abin kwana guda ne? Sannan ka kawo siyasar kabilanci. Ba a taba haka ba...”

- Nyesom Wike

Wike ya ce an jawo fadan kabilanci

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya kaure a wata kasuwar arewa, rayuka 6 sun salwanta

Baya ga zargin sakin layi, Wike ya ce Fubara ya kawo siyasar kabilanci, a cewarsa ba a taba samun rabuwar kabilu irin haka a Ribas ba.

Muddin dokar kasa ta na aiki, tsohon gwamnan kuma jigo a jam’iyyar PDP ya ce ba za a rika fama da matsalar kabilanci a jihar Ribas ba.

Alakar Shugaban kasa Tinubu da Wike

Har yanzu ta ciki na ciki tsakanin Wike da Fubara, ministan ya ce saboda Bola Ahmed Tinubu ne ya tsagaita, ya ajiye kayan fada.

Ministan ya ce ya biyayyarsa ga shugaban ta sa ya bar abubuwa su lafa a rikicin gidan.

Gwamnan adawa ya kare Tinubu

Farfesa Chukwuma Charles Soludo ya ce Muhammadu Buhari ya kashe tattalin arziki kafin ya sauka, a jiya aka kawo wannan rahoto.

Gwamnan yake cewa lokacin da aka mikawa Mai girma Bola Tinubu mulki, an yi raga-raga da kasar,ya zargi CBN da buga kudi barkatai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng