Kotun Daukaka Kara Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Gwamnan PDP, Ta Ba da Dalili
- Kotun daukaka kara raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Delta da ake yi a jihar Legas
- Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna
- Har ila yau, kotun ta yi watsi da karar dan takarar jam'iyyar APC a jihar, Sanata Ovie Omo-Agege
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Delta - Kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta.
Kotun da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
Wane hukunci kotun ta yanke kan zaben Delta?
Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar APC, Sanata Ovie Omo-Agege, Vanguard ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta ce mai karar ba shi da gamsassun hujjoji na rusa zaben da ta bai wa Gwamna Sheriff nasara a watan Maris.
Kafin wannan hukuncin, a watan Satumba kotun zabe ta kori karar Ovie inda ta tabbatar da nasarar Sheriff, Tribune ta ruwaito.
Omo-Agege ya sake rasa dama a kotun daukaka kara
Omo-Agege daga bisani ya daukaka kara zuwa kotun inda ya ke kalubalantar hukuncin karamar kotun, cewar Daily Post.
Sanata Omo-Agege wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ta tara ya bukaci kotun ta yi watsi da hukuncin karamar kotun.
Sheriff shi ne ya tsaya takarar gwamna a jam'iyyar PDP bayan mataimakin dan takarar shugaban kasa a PDP, Okowa ya kammala wa'adinsa.
Kotu ta tabbatar da nasarar Uba Sani na Kaduna
A wani labarin, kotun daukaka kara ta yi hukunci kan shari'ar zaben Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna a yau Juma'a 24 ga watan Nuwamba.
Kotun ta tabbatar da nasarar Uba Sani na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a watan Maris na wannan shekara.
Har ila yau, ta yi fatali da karar dan takarar jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan saboda rashin gamsassun hujjoji.
Asali: Legit.ng