Kano: ’Yan Sanda Sun Tura Gargadi Ga Jam’iyyun APC, NNPP Kan Shirin Zanga-Zanga a Jihar
- Jami’an ‘yan sanda a jihar Kano sun gargadi jam’iyyun APC da NNPP kan shirinsu na yin zanga-zanga a ranar Asabar
- Rundunar ta ce ba ta samu wata takarda dangane da zanga-zangar ba inda ta gargadi jama’a da su guji ta da zaune tsaye
- Kakakin rundunar, Abdullahi Kiyawa shi ya bayyana haka a yau Juma’a 24 ga watan Nuwamba a Kano
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta gargadi masu zanga-zanga kan hukuncin kotun daukaka kara da aka yi a makon jiya.
Rundunar ta tura gargadin ne ga jam’iyyun NNPP da APC yayin da su ka shirya zanga-zanga a ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba.
Yaushe za a yi zanga-zanga a Kano?
Jam’ian ‘yan sanda sun ce za su yi maganin duk wani wanda ke son ta da zaune tsaye yayin zanga-zangar a Kano, Tribune ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, rundunar ta umarci dukkan jam’iyyun da su watsar da wannan shiri da su ke yi na zanga-zangar.
Idan ba a mantaba, jam’iyyun APC da NNPP sun bukaci magoya bayansu su fito don yin zanga-zanga kan hukuncin kotu mai sarkakiya.
Martanin 'yan sanda kan zanga-zangar a Kano
Kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Kiyawa a madadin kwamishinan ‘yan sanda shi ya bayyana haka a yau Juma’a 24 ga watan Nuwamba a Kano.
Ya ce:
“Mun samu bayanai cewa jam’iyyun APC da NNPP na neman hadin kan magoya bayansu don gudanar da zanga-zanga a Kano.
“Mn kuma samu bayanan sirri cewa masu zanga-zangar sun shirya kai hari gidajen wadanda ba sa tare da su wanda hakan zai kawo rudani.
“Don haka runduarmu ba ta samu takarda kan haka ba, kuma duk wanda ya yi zanga-zangar da za ta ta da hankulan jama’a za mu yi maganinshi.”
Kiyawa har ila yau, ya shawarci masu zanga-zangar da su yi ta karkashin doka ba tare da saba duk wani tsari na hukuma ba, cewar Tori News.
APC, NNPP sun shirya yin zanga-zanga a Kano
Kun ji cewa, jam’iyyun APC da NNPP sun shirya gudanar da zanga-zanga a gobe Asabar 25 ga watan Nuwamba.
Wannan na zuwa ne bayan yanke hukuncin kotun daukaka kara a makon da ya gabata.
Asali: Legit.ng