Yan Majalisar Dokoki Sun Shirya Zama, Zasu Dora Mataimaki a Matsayin Gwamnan Jihar APC
- Majalisar dokokin jihar Ondo ta kira zama na musamman ranar Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba, 2023 kan rikicin siyasar jihar
- Rahoto ya nuna mai yiwuwa yan majalisar su ayyana mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa, a matsayin muƙaddashin gwamna
- Suna shirin ɗaukar wannan mataki ne duba da halin da Gwamna Rotimi Akeredolu ke ciki tun bayan dawowa jinya daga Jamus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Mambobin majalisar dokokin jihar Ondo sun shirya zama yau Jumu'a, 24 ga watan Nuwamba, 2023 domin tattauna sarƙaƙiyar siyasar jihar.
An tattaro daga majiya mai tushe cewa ƴan majalisar dokokin zasu fi maida hankali ne kan ɓangaren masu zartarwa na gwamnatin jihar Ondo karkashin gwamna Rotimi Akeredilu.
Matakin da majalisar ke shirin ɗauka
Bayanai sun nuna akwai yiwuwar ƴan majalisar zasu jingine gwamnan gefe guda, su ayyana mataimakin gwamna, Lucky Aiyedatiwa, a matsayin muƙaddashin gwamna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta ce hakan ya biyo bayan gazawar Gwamna Rotimi Akeredolu na komawa ofis tun bayan dawowa daga kasar Jamus sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.
Har yanzu Gwamnan na jam'iyyar APC na ci gaba da murmurewa a gidansa na kai da kai da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Amma wata majiya ta bayyana cewa wasu daga cikin yan majalisar ba zasu halarci zaman yau ba saboda saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan batun Aiyedatiwa.
Uwar jam'iyya ta ƙasa na goyon bayan zaman
Majiyar, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya ce zaman da majalisar zata yi yau Jumu'a ya samu cikakken goyon bayan sakateriyar APC ta ƙasa.
"Yan majalisa sun shirya zama yau kuma ɗaya daga cikin ajendojin da zasu tattauna ita ce ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin muƙaddashin gwamna."
"Duk da wasu ƴan majalisa ba zasu halarta ba saboda ba su goyon bayan Aiyedatiwa ya zama gwamnan riko amma APC ta ƙasa ta san da zaman kuma ta amince," in ji shi.
Yayin da aka tuntubi ɗaya daga cikinsu kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar jihar Ondo, Olatunji Oshati, ya tabbatar da batun zaman da suka tsara yau.
Sai dai ya gaza tabbatar da cewa sun tsara ayyana mataimakin gwamna a matsayin muƙaddashin gwamnan jihar Ondo, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Shugaban PDP na Ribas ya yi murabus
A wani rahoton na daban Awanni bayan Bola Tinubu ya naɗa shi a babban muƙami, shugaban APC na jihar Ribas, Desmond Akawor, ya yi murabus.
A wata takarda da ya aike wa shugaban PDP na ƙasa, Akawor, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan neman shawari daga jagorori da iyalansa.
Asali: Legit.ng