Yanzu: Ministan Tinubu Na Shirin Murabus Yayin da Ya Karbi Shaidar Zama Sanata, Hotuna Sun Fito

Yanzu: Ministan Tinubu Na Shirin Murabus Yayin da Ya Karbi Shaidar Zama Sanata, Hotuna Sun Fito

  • Ga dukkan alamu, ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong zai yi bakwana da majalisar Shugaban kasa Bola Tinubu
  • Hakan ya biyo bayan karbar takardar shaidar cin zaben da ya yi a matsayin sanata mai wakiltar Filato ta Kudu
  • Da farko dai Lalong ya fadi zabe amma sai ya kwato kujerar sanatan daga hannun dan takarar PDP, Napoleon Bali, a kotun zabe da kotun daukaka kara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Simon Lalong, ministan kwadago da daukar ma'aikata, ya karbi takardar shaidar cin zabe a matsayin sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a majalisar dokokin tarayya.

Da farko Lalong, wanda ya yi gwamnan jihar Filato sau biyu, ya fadi zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, inda ya sha kaye a hannun Napoleon Bali na jam'iyyar PDP, kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana.

Kara karanta wannan

APC ta mamaye Majalisar jihar PDP bayan kotu ta kwace dukkan kujeru 16, an shiga yanayi

Lalong ya karbi takardar lashe zaben sanata
Lalong Ya Koma Majalisar Dattawa, Da Yiwuwar Ya Bar Majalisar Tinubu Hoto: Journalist KC
Asali: Twitter

Lalong ya kalubalanci sakamakon zaben, inda ya garzaya kotun sauraron kararrakin zabe kuma ya yi nasara.

Kotun zaben, karkashin jagorancin zaben Mai shari'a Mahmoud Tukur, ta yanke hukuncin cewa kuri’un dan takarar PDP basu da inganci saboda rashin tsayar da shi bisa ka'ida, inda ta ce jam’iyyar ba ta da ingantaccen tsari a jihar a lokacin zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da karar da Bali ya daukaka, kotun daukaka karar karkashin jagorancin Mai shari'a Elfaida Williams-Dawodu, ta tabbatar da hukuncin kotun zaben, inda ta ce kuri’un dan takarar PDP baya bisa doka.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, kotu ta umurci INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe da bayar da sabuwa ga Lalong.

A martaninsu, Lalong da mukarrabansa sun kai ziyara hedikwatar INEC da ke Abuja don karbar takardar shaidar cin zabensa daga hannun kwamishinan hukumar na kasa Mohammed Haruna.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta bayyana ainahin wanda ya lashe zaben gwamnan Kebbi

Wannan mataki na Lalong ya nuna cewa yana iya yin murabus daga mukaminsa na ministan kwadago, matsayin da ke fama da rikice-rikice da yan kwadago, ciki har da yajin aikin da aka yi a fadin kasar sakamakon harin da aka kai wa Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya.

Wani abin mamaki shi ne, lamarin Lalong ya yi kama da na David Umahi, tsohon gwamnan da ya bar majalisar dattawa ya shiga majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu.

Kotu ta tabbatar da zaben gwamnan Nasarawa

A wani labarin, mun ji cewa kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta tabbatar da zaben Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba.

Kotun daukaka karar ta jingine hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wanda ya tsige gwamnan daga kan kujerarsa, jaridar The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng