Kotun Daukaka Kara da Sanya Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kaduna
- Kotun daukaka ta shirya raba gardama a shari'ar da ake yi na zaben gwamnan jihar Kaduna
- Kotun ta sanya gobe Juma'a 24 a watan Nuwamba a matsayin ranar yanke hukuncin shari'ar tsakanin APC da PDP
- Wannan na zuwa ne bayan dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP ya kalubalanci zaben Gwamna Uba Sani
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kotun daukaka kara ta saka ranar yanke hukunci a shari'ar zaben gwamnan jihar Kaduna.
Kotun ta sanya gobe Juma'a 24 ga watan Nuwamba a matsayin ranar raba gardama a shari'ar da ake yi, Legit ta tattaro.
Yaushe kotun za ta yanke hukunci a zaben Kaduna?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da magatakardar kotun ya fitar a kotun shiyya da ke Kaduna, cewar Politics Nigeria.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan na kalubalantar zaben Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC.
A watan Satumba ne kotun zabe ta kori karar dan takarar jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan da ke kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Maris.
Sanarwar hukumar INEC na sakamokon zabe
Kotun har ila yau, ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta ayyana Gwamna Uba Sani a matsayin wanda lashe zaben da aka gudanar a watan Maris.
INEC ta sanar da cewa Gwamna Uba Sani ya samu kuri'u 730,001 inda ya doke abokin hamayyarsa, Isa Ashiru Kudan da ya samu kuri'u 719,196 a zaben.
Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa
A wani labarin, kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC a jihar Gombe.
Kotun ta kuma yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Muhammad Jibrin Barde saboda rashin gamsassun hujjoji.
Kotun ta yi hukuncin ne a yau Alhamis 23 ga watan Nuwamba bayan korar karar Barde a watan Satumbar wannan shekara.
Asali: Legit.ng