Wike Ya Ce Yan Najeriya Suna Murna Kuma Sun Gamsu Da Gwamnatin Tinubu, Ya Bada Dalili

Wike Ya Ce Yan Najeriya Suna Murna Kuma Sun Gamsu Da Gwamnatin Tinubu, Ya Bada Dalili

  • Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da yasa yan Najeriya ke farin ciki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Wike ya ce yan Najeriya na farin ciki dangane da abin da gwamnatin Tinubu ke yi a bangaren sabunta fatan al'umma
  • Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce gwamnatin Tinubu da dukufa wurin farantawa al'umma rai ta hanyar yin abin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesome Wike, ya ce FCTA ta dukufa wurin gina tituna da habaka harkokin tattalin arziki a babban birnin kasar, Abuja.

Ya bayyana hakan ne yayin rangadin duba ayyukan titi da ake yi a birnin tarayyar a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, Vanguard ta rahoto.

Wike ya ce yan Najeriya na farin ciki da Tinubu
Nyesom Wike ya ce yan Najeriya na murna da Tinubu. Hoto: Photo Credit: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki da ya kai kasar Jamus

Wike ya kara da cewa yan Najeriya suna farin ciki kuma sun gamsu da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya yi bayani cewa yan Najeriya na murna domin a yanzu 'fatan alheri' na dawowa ta hanyar shirin 'Sabunta Fata' na Shugaba Tinubu.

"Wannan shine abin da mutane ke so. Ba wai magana ne na fatar baki ba, suna son ganin abu a kasa. Sun cire tsammani, amma yanzu fatansu ya dawo saboda tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Tinubu."

Ministan ya duba aikin babban titin Outer Southern Expressway da ya fara daga A.A. Rano, bayan gidan shugaban kasa ta mahadar Deeper Life, SARS, shataletalen Apo zuwa yankin Wasa da kuma Northern N-2- Expressway a yankin Jahi.

Ya kara da cewa:

"Na ji dadi saboda mutane suna farin ciki kuma sun gamsu da abin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi.
"Ba siddabaru bane; lamari ne na mayar da hankali don gamsar da al'ummarmu. Idan ka yi abin da ya dace, mutane za su yi murna."

Kara karanta wannan

Har yanzu Shugaba Tinubu na jinyar tiyatar da aka aasa a gwiwa, in ji Onanuga

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164