Ana Cikin Zaman Lafiya Ganduje Ya Tono Sabuwar Rigima a Jam'iyyar APC

Ana Cikin Zaman Lafiya Ganduje Ya Tono Sabuwar Rigima a Jam'iyyar APC

  • Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar APC wanda Ganduje ke jagoranta ya tsokano rigima a jihar Rivers
  • Kwamitin ya sauke shugabannin jam'iyyar na jihar inda ya maye gurbinsu da shugabannin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Tony Okocha
  • Sai dai, shugabannin jam'iyyar na jihar sun yi fatali da wannan matakin suna masu cewa sam hakan bai mai yiwuwa ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya sauke shugabannin jam'iyyar na jihar Rivers.

Sai dai, shugabannin jam'iyyar na jihar Rivers sun yi watsi da wannan matakin da kwamitin NWC ya ɗauka na sauke su daga muƙamansu, cewar rahoton Channels tv.

Shugabannin APC a Rivers sun yi watsi da korarsu da NWC ta yi
Shugabannin APC a Rivers sun yi fatali da sauke su daga mukamansu Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Rivers, Emeka Beke, ya musanta sanin labarin cewa uwar jam'iyyar ta ƙasa ta sauke su daga muƙamansu.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruɗani kan tsige Abba Gida-Gida, Ganduje ya kori shugabannin APC na jiha guda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban a daren ranar Laraba ya bayyana cewa:

"Ban ma san da batun saukewar ba amma yanzu bana cikin ƙasar nan. Zan yi magana da ku idan muka samu ƙarin bayani game da batun."

Hakazalika shi ma sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC na jihar, Darlington Nwauju, ya yi watsi da matakin na kwamitin NWC.

Wane mataki shugabannin za su ɗauka?

"Mai ba mu shawara kan harkokin shari’a, shugaban jam'iyyar, da ƴan majalisar zartaswarsa na jiha sun yi watsi da wannan saukewar saboda haramun ne kuma ba za ta tabbata ba." A cewarsa.

Da aka matsa masa kan ko za su je kotu ko a'a, ya ki cewa komai yana mai cewa, hakan zai kawo cikas ga shirinsu idan ya ce wani abu kan hakan.

Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar a zaben 2023, Tonye Cole, da tsohon gwamnan jihar Rotimi Amaechi, ba su ce komai ba kan lamarin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana hanyar da za ta bi domin kwato kujerar gwamnan APC a Arewa

A gefe guda kuma, sabon shugaban kwamitin riƙo wanda kuma ya zama mamba a hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), Tony Okocha, ya ƙi yin magana da manema labarai, yana mai cewa yana jiran a rantsar da shi ranar Juma'a.

Mutanen Wike Sun Samu Shugabancin APC

A wani labarin kuma, kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar APC ya yi waje da shugabannin jam'iyyar APC na jihar Rivers.

Kwamitin ya ɗauko mutanen ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba su shugabancin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng