Kai Tsaye: Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Nasarawa Na 2023

Kai Tsaye: Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Nasarawa Na 2023

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja za ta yanke hukuncinta kan rikicin zaben gwamnan jihar Nasarawa a yau (Alhamis, 23 ga watan Nuwamba).

Kasance tare da Legit Hausa domin samun cikakken bayanin yadda zaman kotun ke gudana kai tsaye.

Kotun daukaka kara ta soke hukuncin da ya tsige Gwamna Sule na Nasarawa

Yanzun nan kotun daukaka karar ta soke hukuncin da ya tsige Gwamna Sule daga kan kujerarsa.

Alkalan kotun guda uku sun amince da cewa kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Nasarawa ta yi kuskure wajen yanke hukuncin cewa Sule bai samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba.

Daga bisani kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin kotun zaben sannan ta tabbatar da zaben Sule a matsayin gwamnan jihar Nasarawa.

Manyan jiga-jigan APC sun isa kotun daukaka kara

Manyan yan siyasa na jam'iyyar APC sun hallara a kotun daukaka kara da ke Abuja don sauraron shari'ar na zaben gwamnan jihar Nasarawa.

Wasu daga cikinsu sun hada da:

  • Tsohon shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu
  • Mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Dr. Emmanuel Akabe
  • Tsohon ministan labarai, Labaran Maku

Yadda kotun zabe ta tsige Gwamna Sule

Ku tuna cewa Kotun zabe ta tsige gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule na jam’iyyar APC.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Sule a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.

A cewar INEC, Sule ya samu jimillar kuri'u 347,209 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa, David Ombugadu,, dan takarar PDP, wanda ya samu kuri'u 283,016.

Sai dai kuma, kotun zabe a hukuncinta, ta tsige Sule na APC daga kujerarsa sannan ta ayyana Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kan haka ne Sule ya tunkari kotun daukaka kara don neman hakkinsa.

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng