Adamu, Al-Makura da Labaran Maku Sun Dira Kotu Gabanin Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Nasarawa
- Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun isa kotun daukaka kara a Abuja don sauraron shari'ar zaben gwamnan jihar Nasarawa
- Manyan masu fada aji cikinsu sun hada da tsohon shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu; mataimakin gwamnan Nasarawa, Emmanuel Akabe da tsohon minista Labaran Maku
- Hakazalika tsohon darakta janar na hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, Mike Omeri, ya hallara a kotun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Lafia, jihar Nasarawa - Abdullahi Adamu, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, sun hallara a kotun daukaka kara yayin da za a yanke hukunci kan rikicin zaben gwamnan jihar a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba.
Legit Hausa ta rahoto cewa Adamu ma ya kasance tsohon gwamna a jihar Nasarawa.
Baya ga Adamu da Al-Makura, Labaran Maku, tsohon ministan labarai, da Silas Ali Agara, mataimakin gwamnan jihar Nasarawa mai ci duk sun hallara a kotun daukaka karar, gabannin yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Channels TV ya lura da kasancewar manyan jiga-jigan yan siyasar daga jihar ta yankin arewa ta tsakiya a kotun.
Ga bidiyo da hotunan zaman a kasa:
Kotun daukaka kara ta Nasarawa zata yanke hukunci
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa kotun ɗaukaka ƙara mai zama a birnin tarayya Abuja ta tsaida ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023 a matsayin ranar yanke hukunci a shari'ar zaɓen gwamnan jihar Nasarawa.
Kotun zata raba gardama ne tsakanin Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC da kuma David Ombugadu na jam'iyyar PDP, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.
Idan baku mance ba ranar 15 ga watan Nuwamba, kotun ɗaukaka ƙara ta tanadi hukuncinta a ƙarar da Gwamna Sule ya shigar gabanta yana kalubalantar hukuncin kotun zaɓe.
Malamin addini ya shawarci dan takarar PDP
A wani labarin kuma, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya buƙaci David Ombugadu, ɗan takarar jam'iyyar PDP a jihar Nasarawa, da ya sa ido sosai yayin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar.
Ayodele ya buƙaci ɗan takarar na jam'iyyar PDP da kada ya yi wasa a ƙoƙarin da ya ke yayin da ake jiran hukuncin da kotun ɗaukaka ƙarar za ta yanke.
Asali: Legit.ng