Abubuwa 2 Na Sani Yayin da Kotun Daukaka Kara Ke Yanke Hukunci Kan Soke Zaben Gwamnan Nasarawa

Abubuwa 2 Na Sani Yayin da Kotun Daukaka Kara Ke Yanke Hukunci Kan Soke Zaben Gwamnan Nasarawa

Jihar Nasarawa: Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta sanar da cewa za ta yanke hukunci kan ƙarar da gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya shigar kan hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar na soke zaɓensa.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

A ranar 2 ga watan Oktoba ne kotun zaɓen ta kori Gwamna Sule na jam’iyyar APC a zaɓen, inda ta bayyana David Ombugadu na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Kotu za ta raba gardama kan shari'ar gwamnan Nasarawa
A yau kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Nasarawa Hoto: Abdullahi Sule, David Ombugadu
Asali: Twitter

Yadda Kotu ta kori Gwamna Sule na Jihar Nasarawa

Mai shari’a Ezekiel Ajayi, shugaban kotun mai alƙalai uku, a hukuncin da ya yanke, wanda aka yanke ta hanyar Zoom, ya bayyana cewa Ombugadu da PDP sun kare ƙarar da suka shigar a gaban kotun, don haka suka soke zaɓen gwamnan.

Kara karanta wannan

Tsige gwamnan Kano: Kotun daukaka kara ta bukaci lauyoyi su dawo da takardun hukuncin da ta yanke

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kotun, alƙalai biyu sun amince cewa APC ba ta ci zaɓen ba yayin da alƙali na ukun ya saɓa daga ra'ayinsu.

Daga baya Gwamna Sule da jam'iyyar APC sun shigar da ƙara kan hukuncin kotun zaɓe kuma kotun ɗaukaka ƙara ranar Laraba 22 ga watan Nuwamba ta sanar da lauyoyin da ke cikin ƙarar cewa za a yanke hukunci a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba.

Sai dai, gabanin yanke hukuncin, abubuwa da dama sun faru a jihar. Ga manya daga cikinsu an jero a ƙasa:

Ƴan sanda sun gargadi magoya bayan PDP da APC gabanin yanke hukunci a kotu

Gabanin hukuncin kotun dai an samu rahotannin tashin hankali da fargaba daga magoya bayan APC da PDP. Dukkanin ɓangarorin biyu suna fatan samun sakamako mai kyau daga kotun ɗaukaka ƙarar.

A sakamakon hakan ne rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta ja kunnen magoya bayan jam'iyyar PDP da APC kan ta da zaune tsaye, sannan ta yi kira ga al'ummar jihar da su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum da kuma bin doka da oda.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnoni 3, Kotun daukaka kara ta tsaida ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan APC

Magoya bayan PDP sun koma ga Allah

Haka kuma, an ruwaito cewa magoya bayan jam'iyyar PDP sun gudanar da azumi da addu'o'i na kwana bakwai a kan gwamnan da jam’iyyar APC a jihar, cewar rahoton The Punch.

Suleiman Abdullahi, ɗaya daga cikin jagororin shirya addu'o'in da ya zanta da manema labarai a Lafiya, ya bayyana fatansa na ganin cewa jama’a za su samu adalci a kotun ɗaukaka ƙara.

Wani ɓangare na bayaninsa na cewa:

"Allah shi ne mahaliccin talikai. Ba ya nuna bambanci ko gazawa a cikin alƙawuransa. Don haka yunƙurin sauya fatan jama'a domin ba wadanda suke so ba zai yiwu ba."

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tanadi Hukunci

A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta tanadi hukunci kan ƙarar da Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya shigar bayan kotun zaɓe ta tsige sho.

Kotun zaɓen dai ta soke zaɓen Gwamna Sule na jam'iyyar APC inda ta bayyana ɗan takarar PDP, David Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng