Daga Karshe Kotun Daukaka Kara Ta Fitar da Muhimman Takardu Kan Hukuncin Shari'ar Gwamnan Kano
- Kotun ɗaukaka ƙara ta fitar da takardun hukuncin shari'ar zaɓen gwamnan Kano da ta yanke a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba
- Salihu Tanko Yakasai da Abdulaziz Na'ibi Abubakar su ne suka sanya takardun na CTC a shafukansu na X
- Fitar da takardun dai na zuwa ne bayan jam'iyyar NNPP ta koka kan cewa kotun ɗaukaka ƙarar ta ƙi fitar da takardun
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Kwanaki biyar bayan yanke hukunci, kotun daukaka ƙara ta saki takardun hukuncin shari'ar gwamnan Kano da ta yanke.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke hukuncin ne a kan zaɓen gwamnan jihar Kano da ake takaddama a kai a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba, inda ta ba jam'iyyar APC da ɗan takararta, Nasiru Gawuna, nasara.
Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi sani da Dawisu, ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam'iyyar PRP a zaɓen 2023 ne ya sanya takardun na CTC a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin yanzu Dawisu jigo ne a jam’iyyar APC kuma na hannun daman Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.
Kotun ɗaukaka ƙara ta fitar da takardun CTC
Ya rubuta a yammacin ranar Talata, 21 ga Nuwamba, tare da takardun na CTC cewa:
"Kotun ɗaukaka ƙara ta bambanta ƙararrakin biyu; Peter Obi da na Kano APC da NNPP. Shafuffuka na 64 zuwa 67 sun yi bayani tare da hujjoji don tabbatarwa. Kasancewar mamba a jam'iyya na iya zama al'amarin gabanin zaɓe da kuma na bayan zaɓe. Ina fatan wannan zai sa wannan ya kawo ƙarshen taƙaddamar."
Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar, jigo a jam'iyyar PDP, shi ma ya sanya takardun na CTC a shafinsa na X.
Sakin takardun na CTC na zuwa ne kwana guda bayan da muƙaddashin shugaban jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya koka kan gazawar kotun ɗaukaka ƙara na sakin takardun CTC na shari’ar Kano.
Ali ya yi zargin cewa akwai ƙoƙarin da ake yi da gangan domin kawo wa NNPP cikas.
Obasanjo Ya Magantu Kan Tsige Gwamnoni
A wani labarin kuma, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan yadda kotu na ke tsige gwamnoni a ƙasar nan.
Obasanjo ya yi nuni da cewa bai kamata alƙalai uku kacal su sauya zaɓin da miliyoyin ƴan Najeriya suka yi a lokacin zaɓe ba.
Asali: Legit.ng