Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Hanyar da Za Ta Bi Domin Kwato Kujerar Gwamnan APC a Arewa

Jam'iyyar PDP Ta Bayyana Hanyar da Za Ta Bi Domin Kwato Kujerar Gwamnan APC a Arewa

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba ta saduda ba kan ƙudirinta na karɓe kujerar gwamnan Benue daga hannun jam'iyyar APC
  • PDP a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na jihar ya yi ta bayyana cewa za ta cigaba da bin matakan shari'a domin ƙwato nasararta a kotu
  • Jam'iyyar ta yi nuni da cewa ko tantama ba ta yi ɗan takararta na gwamna shi ne wanda ya lashe zaɓen na ranar 18 ga watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - A ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba jam'iyyar PDP a jihar Benue ta jaddada ƙudirinta na bin hanyar da doka ta tanada domin kwato kujerar gwamnan jihar.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar na jihar Bemgba Iortyom, a wata sanarwa da ya fitar a Makurdi, ya yi iƙirarin cewa cimma ƙudirin ya biyo bayan imanin da PDP ta yi na cewa kujerar ta jam'iyyar ce, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Atiku Abubakar ya maida martani mai zafi kan tsige gwamnonin arewa biyu

PDP na son kwace kujerar Gwamna Alia
Jam'iyyar PDP na son kwace kujerar Gwamna Hyacinth Alia Hoto: Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Martanin na PDP ya biyo bayan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba a Abuja wacce ta yi watsi da karar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar, Engr. Titus Uba, ya shigar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar ya shigar da ƙarar ne bayan ya ƙi amincewa da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar, wanda ya tabbatar da nasarar Gwamna Hyacinth Alia na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen 2023.

Wane fata jam'iyyar PDP ke da shi?

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Abin da jam’iyyar PDP ke jayayya a kai bisa ga dokoki da ƙa'idojin zaɓe, kujerar gwamnan jihar a zaɓen da ya gabata Engr. Titus Uba ne ya lashe ta kamar yadda lauyoyinsa suka nuna a kotun zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara."
"Shugabannin jam’iyyar za su tuntuɓi tawagar lauyoyi kan hanyar da ta dace kan mataki na gaba a shari’ar, sannan ta buƙaci ƴayanta da magoya bayanta da su cigaba da yin imani da cewa ba shakka za a yi adalci kan ƙarar da Engr. Titus Uba ya shigar."

Kara karanta wannan

Bayan Kano, Mataimakin Shugaban APC ya faɗi kujerar gwamnan da zasu ƙwace a arewa

Ya bayyana cewa jam'iyyar ta yi amanna cewa shari'a ita ce hanyar ƙarshe ga ƴan ƙasa wajen samun ƙwato haƙƙinsu da aka ƙwace.

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Alia

A wani labarin kuma, kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta tabbatar da nasarar Gwamna Hyacinth Alia na jam'iyyar APC.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta Engr. Titus Uba suka shigar suna ƙalubalantar nasarar gwamnan a zaɓen na ranar 18 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng