Ba Bayin Ka Ba Ne Mu, Sanatoci Sun Yi Wa Akpabio Rashin Kunya Kan Dalili 1 Tak, Ya Yi Bayani

Ba Bayin Ka Ba Ne Mu, Sanatoci Sun Yi Wa Akpabio Rashin Kunya Kan Dalili 1 Tak, Ya Yi Bayani

  • Tashin hankali yayin da Godswill Akpabio ya shiga matsi bayan zarginshi da baba-kere
  • Mambobin Majalisar daga bangaren jam'iyyun adawa sun zargi Akpabio da zaba musu shugabanni da ba sa so
  • Wannan na zuwa ne bayan zabar Abba Moro daga PDP a matsayin shugaban marasa rinjaye a Majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An samu hargitsi a fadar Majalisar Dattawa yayin zaban shugabannin marasa rinjaye.

Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio shi ya jagoranci zaman a yau Talata 21 ga watan Nuwamba a Abuja, Premium Times ta tattaro.

Sanatoci marasa rinjaye sun soki Akpabio da son kakaba musu shugabanni
An samu hargitsi a Majalisar Dattawa kan zaben shugabanni. Hoto: Godswill Akpabio.
Asali: Facebook

Wane dalili ne ya jawo hargitsin a Majalisar?

Zaban shugabannin marasa rinjayen na zuwa ne bayan korar mambobin Majalisar daga kujerunsu da kotu ta yi.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fayyace ainihin sababin tsige Abba, gwamnan Filato a Kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta kwace kujerar Sanata Simin Davou daga PDP a mai wakiltar Plateau ta Arewa da Darlington Nwokocha daga LP wanda shi ne mai tsawatarwa na marasa rinjaye.

Yayin zaban wadanda za su shugabanci kujerun, Akpabio ya sanar da Abba Moro daga PDP mai wakiltar Benue ta ta Kudu a matsayin shugaban marasa rinjaye.

Ya kuma sanar da Osita Ngwu daga PDP mai wakiltar Enugu ta Yamma a matsayin mai tsawatarwa na marasa rinjaye.

Wane martani mambobin su ka yi kan zaben?

Yayin da ya ke korafi, Sanata Okechukwu Ezea daga LP mai wakiltar Enugu ta Arewa ya ce wannan tsantsar rashin adalci ne.

Ya ce:

"Ta yaya PDP za ta dauki kujerun marasa rinjaye har guda uku, wannan rashin adalci ne."

Har ila yau, Tony Nwoyi daga LP mai wakiltar Anambra ta Arewa ya zargi Akpabio da mayar da su bayinsa, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dalilai 4 da suka sa Anyanwu na PDP ya fadi zaben gwamnan Imo na 2023

Ya ce:

"Ta yaya za ka zaba mana shugabanninmu, an fada maka mu bayin ka ne."

Akpabio ya gargadi shugaban EFCC

A wani labarin, shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya gargadi shugaban EFCC, Ola Olukoyede kan misali da sunanshi.

Akpabio ya bayyana haka ne yayin tantance Ola a fadar Majalisar bayan Shugaba Tinubu ya nada shi mukamin shugaban hukumar.

Wannan na zuwa ne yayin da Ola ke misali da sunan Akpabio a yaki da cin hanci a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.