Shari’ar Gwamnan Adamawa: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasar Ahmadu Fintiri Na PDP

Shari’ar Gwamnan Adamawa: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasar Ahmadu Fintiri Na PDP

  • Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan Adamawa a zaben jihar da ya gabata
  • Kotun ta yi watsi da daukaka karar da dan takarar SDP, Dakta Umar Ardo ya shigar, na kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben jihar
  • Ardo ya bukaci a soke nasarar Gwamna Fintiri bisa dalilai da suka shafi almundahana da karya dokokin zabe, sai dai kotun ta ce ba ta samu kwararan hujjoji ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Adamawa - Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP, Dakta Umar Ardo, ya shigar kan nasarar zaben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Kano: Jigon NNPP ya tona asirin hanyar da APC ke bi don mayar da jihar karkashin ikonta saboda 2027

Bayan sanar da Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna, Ardo ya tunkari kotun inda ya nemi ta soke zaben Fintiri bisa dalilin rashin bin dokokkin da hukumar zabe ta sanya a zaben jihar.

Gwamna Ahmadu Fintiri
Kotun Daukaka Karar ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri tare da yin watsi da bukatar dan takarar SDP na soke zaben jihar Hoto: Ahmadu Fintiri
Asali: Twitter

Sai dai shugaban kotun, Mai Shari’a T. O. Uloho, ya yi watsi da karar saboda rashin hujjoji da kuma rashin shigar da karar ta hanyar da ya dace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yi watsi da daukaka karar Dakta Ardo na SDP

Jaridar The Whistler ta ruwaito cewa Ardo bai gamsu da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben ba, inda ya garzaya Kotun Daukaka Kara don neman ayi masa adalci.

A hukuncin da ya yanke a ranar Talata, Mai shari’a Ugochukwu Ogaku na Kotun Daukaka Kara ya amince da hukuncin kotun kararrakin zaben, inda ya ce wadanda suka shigar da karar ba su tabbatar da zargin almundahana da rashin bin dokar zabe a kan INEC ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta tsige gwamnan Filato, alkalai sun ce APC ta ci zaben 2023

Ya ce babu wata hujja da za ta gamsar da Kotun Daukaka Karar, jaridar The Cable ta ruwaito.

"Wannan karar ba ta da inganci, kuma wannan kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun kararrakin zabe ta yanke na yin watsi da karar da jam'iyyar SDP da dan takararta suka shigar,"

- Cewar kotun.

Kotu ta yanke hukunci kan nasarar Gwamna Fintiri na jihar Adamawa

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta kara tabbatar da nasarar Gwamna Ahmadu Umar Fintiri na jiha Adamawa, Legit Hausa ta ruwaito.

Da take yanke hukunci ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, 2023, shugaban kwamitin alkalan Kotun mai shari'a Theodora Uloho, ta kori karar bisa rashin cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.