Shugaba Tinubu Ne Ya Sa Kotu Ta Tsige Abba Gida-Gida da Gwamnonin PDP 2? Gaskiya Ta Fito Daga Villa

Shugaba Tinubu Ne Ya Sa Kotu Ta Tsige Abba Gida-Gida da Gwamnonin PDP 2? Gaskiya Ta Fito Daga Villa

  • Fadar shugaban ƙasa ta maida martani kan kalamam Atiku Abubakar da PDP dangane da gwamnonin da Kotun ɗaukaka ƙara ta tsige
  • A wata sanarwa da Bayo Onanuga ya fitar ranar Litinin, ta ce Shugaba Tinubu ba ya tsoma baki a harkokin ɓangaren shari'a
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya yi zargin cewa Tinubu na kokarin maida Najeriya ƙasar jam'iyya ɗaya tal

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ba ya tsoma baki a bangaren shari’a dangane da hukuncin da kotuna suka yanke kan sakamakon zaben 2023.

Atiku Abubakar da shugaban kasa, Bola Tinubu.
"Ba ruwan Tinubu da harkokin shari'a" Fadar shugaban kasa ta maida martani ga Atiku Hoto: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Fadar shugaban ƙasa ce ta bayyana haka a wata sanarwa, inda ta musanta zargin cewa Tinubu na ƙoƙarin maida ƙasar nan ta jam'iyya ɗaya tal.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Atiku Abubakar ya maida martani mai zafi kan tsige gwamnonin arewa biyu

Fadar shugaban ta yi wannan ƙarin hasken ne domin martani ga zargin jam'iyyar PDP da ɗan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, wadanda ke ganin APC na shirin kwace komai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu hukunce-hukuncen da kotun daukaka kara ta yanke a baya-bayan nan kan sakamakon zaben 2023 sun yi wa APC dadi yayin ta bar yan adawa musamman PDP cikin ƙunci.

Shugaba Tinubu ba ya katsalandan a harkokin shari'a

Sai dai fadar shugaban ƙasa ta karyata zargin da Atiku ya yi cewa APC na shirin maida Najeriya kasar jam'iyya ɗaya a wata sanarwa da Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa ranar Litinin.

Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru ya yi kira ga PDP da Atiku su guji kalaman ƙarya game da hukuncin kotu.

Sanarwan ta ƙara da cewa da gangan aka kirkiro wannan zargin da nufin, "zafafa al'amuran siyasa da kuma tada hankula a ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Yadda Atiku da Obi za su kayar da Tinubu a zaben 2027

"Atiku da jam’iyyarsa sun kasa bayani kan ko sun yi wani bincike mai zurfi kafin su fito fili suna zarge-zarge masu nauyi, zage-zage, da rashin gaskiya."
"Shugaba Tinubu cikakken ɗan demokuraɗiyya ne kuma muna da ƙarfin guiwar da zamu fito mu bayyana cewa ba ya tsoma baki a hukuncin da kotu ta yanke."

- Bayo Onanuga.

Hadimin Atiku ya caccaki INEC

A wani rahoton na daban Daniel Bwala, ɗaya daga cikin na hannun daman Atiku ya caccaki hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) kan zaben 2023.

Tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku/Okowa na PDP ya ce INEC ce babbar matsalar da ta lalata zaɓen da ya wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262