"INEC Ce" Tsohon Kakakin Kwamitin Kamfen Atiku Ya Gano Babbar Matsalar da Aka Samu a Zaben 2023
- Daniel Bwala, ɗaya daga cikin na hannun daman Atiku ya caccaki hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) kan zaben 2023
- Tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku/Okowa na PDP ya ce INEC ce babbar matsalar da ta lalata zaɓen da ya wuce
- A cewarsa, INEC ce za ta tantance kuma ta amince da takardu amma daga baya ta shiga Kotu tana kalubalantar waɗannan takardu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon kakakin kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na PDP a 2023, Daniel Bwala ya caccaki hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC).
Wace matsala aka samu a zaɓen 2023?
Bwala ya ayyana hukumar zaɓe INEC a matsayin babbar matsalar da aka fuskanta a zaben da ya gabata na 2023 a dukkan matakai tun daga sama har kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon kakakin kwamitin kamfen Atiku/Okowa ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidan talabijin na Channels cikin shirin siyasa a yau ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba.
A kalamansa, Bwala ya ce:
"Babban mai laifi, babbar matsalar da aka fuskanta a zaben 2023 na dukkan matakai, ita ce INEC saboda mun ga sirrin hukumar zaɓe mai wahalar fahimta."
"A wannan zaɓen na 2023 da ya wuce, INEC ce za ta tantance takardun da kuka miƙa mata kuma ta koma gaban Kotu daga baya ta nuna sam ba ta amince da takardun ba, sannan ita kotun ba ta gargaɗe ta ba."
"Saboda haka muna fatan wata rana duk zamu tsallake wannan kwan-gaba kwan-baya, amma dai wannan zaɓen ya bar darussa masu ɗumbin yawa."
Wannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin tsige gwamnonin jam'iyyar PDP guda biyu.
A jihar Filato, Kotun ta ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya ci zaɓe yayin da ta umarci a sake zaɓe a wasu kananan hukumomin jihar Zamfara.
Da yake tsokaci kan tsige gwamnan jihar Filato, Daniel Bwala ya ce bai taɓa ganin inda aka soke zaɓe kan ƙin bin umarnin kotu ba, Vanguard ta ruwaito.
Atiku Abubakar Ya Maida Martani Mai Zafi
Kuna da labarin Alhaji Atiku Abubakar ya yi Alla wadai da hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara na tsige wasu gwamnonin jam'iyyar adawa.
Atiku, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya zargi APC mai mulki da gurgunta tsagin adawa da kuma jefa dimokuradiyya cikin hadari a kasar nan.
Asali: Legit.ng