Gwamnan Plateau Ya Dauki Mataki Na Gaba Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Shi
- Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya ce hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na soke zaɓensa koma baya ne na wucin gadi
- Mutfwang ya bayyana fatansa cewa za a mayar masa da nasarar da ɗaukacin jama'ar Plateau suka ba shi
- A cewarsa, ya umurci tawagar lauyoyinsa da su shigar da ƙara kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a kotun ƙoli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jos, jihar Plateau - Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau, ya bayyana hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na soke zaɓensa a matsayin koma baya na wucin gadi.
Gwamnan ya sha alwashin cewa hukuncin ba zai hana shi mayar da jihar kan turbar zaman lafiya, haɗin kai, da cigaba ba, kamar yadda jaridar Channels tv ta ruwaito a ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba.
PDP vs APC: Halin da ake ciki a Plateau yayin da kotun daukaka kara ke yanke hukunci kan zaben gwamna
A ranar Lahadi, 19 ga watan Nuwamba kotun ɗaukaka ƙara ta tsige Gwamna Mutfwang inda ta tabbatar da ɗan takarar APC, Nentawe Yilwatda a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane mataki Gwamna Mutfwang ya ɗauka?
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa, ya umurci tawagar lauyoyinsa da su shigar da ƙara a kotun ƙoli.
Gwamnan ya bayyana matakin da zai ɗauka na gaba ta hanyar wata sanarwa da Gyang Bere, daraktansa na yaɗa labarai da hulda da jama'a ya fitar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Shi (Mutfwang) ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a mayar da nasarar da jama’ar jihar Plateau suka ba shi, kamar yadda ya umurci tawagar lauyoyinsa da su shigar da ƙara a kotun ƙoli."
Jaridar Business Day ta ruwaito cewa Mutfwang ya bayyana ƙwaƙƙwaran fatansa kan kiyayewa da kare nasararsa, yana mai jaddada amincewarsa ga tsarin shari'a.
Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Plateau
A wani labarin kuma, an samu ɓarkewar zanga-zanga a wasu sassan birnin Jos, babban birnin jihar Plateau, biyo bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige Gwamna Caleb Mutfwang na jam'iyyar PDP.
Wasu magoya bayan jam'iyyar PDP waɗanda hukuncin bai yi wa daɗi ba, sun fito domin nuna adawarsu da hukuncin kotun na raba Gwamna Mutfwang da kujerar gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng