Cikakkun Jerin Jihohin da ke Karkashin Ikon APC, PDP Bayan Zabukan Kogi, Bayelsa da Imo
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Al'ummar jihohin Imo, Kogi da Bayelsa sun yi tururuwan fitowa a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba domin zaben yan takarar da suke muradi a matsayin gwamnoninsu.
Bayan kammala zabe da tattara sakamako, Gwamna Hope Uzodimma na APC ya sake zarcewa a karo na biyu a jihar Imo, haka kuma Gwamna Duoye Diri na PDP a jihar Bayelsa.
Alhaji Usman Ododo na APC shine ya lashe zaben gwamna a jihar Kogi kuma za a rantsar da shi a watan Janairun 2024 bayan cikar wa'adin mulkin Gwamna Yahaya Bello.
Bayan kammala zabukan ciko na gwamnoni, ga jerin jihohi da jam'iyyar APC mai mulki, PDP, Labour Party da sauransu ke iko a cikinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudu maso Gabas
Alex Otti (Abia) Labour Party
Dan takarar jam'iyyar Labour Party mai shekaru 58 ya samu gagarumin nasara a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 16 ga watan Maris.
Tsohon Manajan Darakta na Bankin Diamond ya sha kaye a zaben gwamnan a 2015 da 2019, Channels TV ta rahoto.
Francis Nwifuru (Ebonyi): APC
Nwifuru ya kasance kakakin majalisar dokokin jihar Ebonyi sau biyu. Mutumin mai shekaru 48 ya fito ne daga Oferekpe Agbaja a karamar hukumar Izzi ta jihar.
Peter Mbah (Enugu) PDP
Da siyasar mai shekaru 51, shi ne wanda ya kafa kuma shugaban kamfanin Pinnacle Oil and Gas Ltd. Ya kuma kasance lauya kuma mai sharhi kan harkokin kudi. Ya fito daga Owo a karamar hukumar Nkanu ta Gabas
Hope Uzodimma (Imo) APC
Ya kasance sanata mai wakiltan Imo ta Yamma tsakanin 2011 da 2019.
Charles Soludo (Anambra) APGA
Dan siyasar mai shekaru 63 ya kasance ma'aikacin banki kuma farfesa a fannin tattalin arziki a jami'ar Najeriya.
Soludo ya kasance tsohon gwamna kuma shugaban kwamitin gudanarwa na babban bankin Najeriya.
Kudu maso Kudu
Umo Eno (Akwa Ibom) PDP
Dan siyasar mai shekaru 59 ya yi aiki a matsayin kwamishinan filaye da albarkatun ruwa na jihar Akwa Ibom.
Bassey Otu (Cross River) APC
Ya kasance tsohon dan majalisar wakilai wanda ya wakilci Calabar Municipal/Odukpan kuma Sanata mai wakiltar Cross River ta Kudu.
Sheriff Oborevwori (Delta): PDP
Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Delta daga 2017 zuwa 2023. Dan siyasar mai shekaru 60 ya wakilci mazabar Okpe yayin da yake majalisa.
Siminalayi Fubara (Rivers): PDP
Fubara ya kasance tsohon akanta janar na jihar Rivers. Gwamnan ya fito ne daga Garin Opobo a karamar hukumar Opobo/Nkoro.
Godwin Obaseki (Edo) PDP
Obaseki ya kasance Shugaban tawagar Tattalin Arziki da Dabaru ta Jihar Edo a karkashin gwamnatin Adams Oshiomhole.
Ya yi aiki a matsayin mamba na kwamitin zartarwa na kamfanoni masu zaman kansu da dama ciki har da Afrinvest.
Douye Diri (Bayelsa) PDP
Dan siyasar mai shekaru 64, ya kasance sanata mai wakiltar Bayelsa ta tsakiya daga 2019 zuwa 2020 a majalisar dokokin tarayya ta 9.
Kudu maso yamma
Babajide Sanwo-Olu (Lagos) APC
Dan siyasar mai shekaru 57 ya kasance tsohon shugaban hukumar raya kadarori na jihar Legas.
Dapo Abiodun (Ogun): APC
Dan siyasar mai shekaru 62, shi ne ya kafa kamfanin First Power Limited kuma ya yi aiki a matsayin manajan darakta na Heyden Petroleum.
Abiodun shi ne tsohon shugaban hukumar kula da harkokin kamfanoni (CAC).
Seyi Makinde (Oyo) PDP
Gwamnan mai shekaru 55 ya kafa kamfanin Makon Engineering and Technical Services (METS) a lokacin yana da shekaru 29 a cikin 1997
Ya fadi zaben gwamna a 2015 a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP)
Rotimi Akeredolu (Ondo) APC
Gwamnan mai shekaru 67, ya kasance babban Lauyan Najeriya (SAN) kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) a shekarar 2008.
Abiodun Oyebanji (Ekiti) APC
Dan siyasar mai shekaru 56 ya kasance tsohon sakataren gwamnatin jihar Ekiti kuma tsohon shugaban ma'aikata.
Ademola Adeleke (Osun) PDP
Gwamnan mai shekaru 63 ya kasance tsohon Sanata mai wakiltar Osun ta Yamma daga 2017 zuwa 2019 a Majalisar Tarayya Abuja.
Arewa ta Tsakiya
Rabaran Hyacinth Alia (Benue) APC
An zabi limamin cocin katolikan a ranar 19 ga watan Maris karkashin jam'iyyar APC mai mulki.
Dan siyasar mai shekaru 49 a duniya ya kasance dan majalisar wakilai a shekarar 2011. Ya kammala karatunsa a jami’ar Fasaha ta Tarayya ta Minna. ya shafe shekaru a matsayin ma’aikacin banki kafin ya shiga harkokin siyasa.
Caleb Mutfwang (Plateau): PDP
Gwamnan jihar Filato mai ci a yanzu ya kasance dan siyasa ne mai shekaru 58. Mutfwang ya kasance tsohon shugaban karamar hukumar Mangu.
AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara): APC
Kafin nasararsa a shekarar 2015, dan siyasar mai shekaru 63 ya sha kaye a zaben gwamna tsakanin 2007 da 2011 a karkashin jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC).
Abdullahi Sule (Nasarawa) APC
Wanda ya kafa kamfanin mai na Sadiq Petroleum Nigeria Limited kuma daga baya ya zama shugaban kamfanin African Petroleum (AP) Plc a shekarar 2001.
An nada shi Babban Manajan Darakta na kamfanin sikari na Dangote kafin ya zama gwamna a 2019.
Zababben gwamna Usman Ododo (Kogi) APC
Gogaggen ma'aikacin bankin shi ne tsohon babban mai binciken kananan hukumomi.
Ododo zai karbi ragamar mulki daga hannun gwamna mai ci Yahaya Bello, wanda ya fito daga jam’iyyar APC mai mulki.
Arewa maso Yamma
Umar Namadi (Jigawa): APC
Akantan ya kasance tsohon mataimakin gwamna kuma wanda ya assasa kamfanin Namadi, Umar & Co.
Shi ne shugaban sashen kula da asusun rukunin kamfanonin Dangote.
Uba Sani (Kaduna): APC
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya kuma mataimakin shugaban masu faftukar dimokradiyya na kasa (Arewa).
Gwamnan mai shekaru 52 ya karbi ragamar mulki daga hannun Mallam Nasir El-Rufai.
Abba Yusuf (Kano): NNPP
Dan siyasar mai shekaru 60 ya kasance tsohon kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri. Injiniyan shine gwamnan NNPP na farko a Najeriya.
Dikko Radda (Katsina) APC
Dan siyasar mai shekaru 53 ya kasance tsohon sakataren walwala na APC na kasa, ya kuma taba rike mukamin darakta-janar na hukumar SMEDAN kafin ya karbi mulki daga hannun Aminu Masari.
Nasir Idris (Kebbi) APC
Gwamnan mai shekaru 57 a duniya shi ne shugaban kungiyar malamai na Najeriya. Idris ya kuma kasance mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya.
Ahmad Aliyu (Sokoto): APC
Aliyu tsohon mataimakin gwamna ne kuma kwamishina a jihar Sokoto. Gwamnan mai shekaru 53 ya kuma yi aiki a matsayin babban akanta a ma’aikatar kula da ayyukan kananan hukumomi da kuma babban sakataren hukumar yan sanda.
Dauda Lawal (Zamfara): PDP
Gwamnan mai shekaru 57, ya kasance tsohon gwamnan babban bankin kasa, mai ba Lamido Sanusi shawara na musamman kan harkokin bankin Musulunci.
Gogaggen ma’aikacin bankin ya yi digirin digirgir a fannin kasuwanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.
Arewa ta Gabas
Kefas Agbu (Taraba): PDP
Dan siyasar mai shekaru 52, ya kasance Laftanar kanar na soja mai ritaya.
Agbu ya kasance tsohon shugaban hukumar gudanarwar na NIMASA kuma mamba a kwamitin shugaban kasa kan shirin Arewa maso Gabas (2016-2019).
Ahmadu Fintiri (Adamawa) PDP
Gwamnan mai shekaru 55 ya rike mukamin mukaddashin gwamna daga watan Yuli zuwa Oktoban 2014 a lokacin da aka tsige Gwamna Murtala Nyako.
Kafin wannan lokacin, Fintiri ya kasance kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa.
Bala Mohammed (Bauchi) PDP
Gwamnan mai shekaru 64, ya kasance tsohon ministan babban birnin tarayya (FCT) kuma Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a majalisar dokokin kasar.
Mohammed ya kuma yi aiki a matsayin Babban Jami’in Gudanarwa a Fadar Shugaban Kasa daga 1994 zuwa 1995.
Babagana Zulum (Borno) APC
Zulum ya kasance Farfesa kuma tsohon shugaban riko na tsangayar aikin injiniya a jami'ar Maiduguri.
Inuwa Yahaya (Gombe) APC
Gwamnan mai shekaru 61, ya taba rike mukamin kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arziki.
Inuwa yayi aiki a matsayin manajan darakta na kamfanin A.Y.U Civil Engineering Company Ltd kafin ya shiga harkar siyasa a shekarar 1999.
Mai Mala Buni (Yobe) APC
Dan siyasar mai shekaru 55, shine zababben sakataren jam’iyyar APC na kasa na farko.
Buni ya kuma zama shugaban riko na jam’iyyar (2020-2022) bayan korar Adam Oshiomhole.
Kotu ta tsige gwamnan Filato
A wani labarin kuma, mun ji cewa kotun daukaka kara ta gabatar da hukunci a shari’ar zaben gwamnan Filato wanda ya gudana a farkon shekarar nan ta 2023.
Leadership ta rahoto cewa Alkalan kotun daukaka kara sun tabbatar da jam’iyyar APC ce ta lashe zaben gwamnan jihar na Filato.
Asali: Legit.ng