Kotu Ta Tsige Gwamnan Filato, Alkalai Sun Ce APC Ta Ci Zaben 2023
- Kotun daukaka kara tayi watsi da nasarar da kotun sauraron korafin zabe ta ba Gwamnan Filato
- Kafin zabe an bukaci PDP ta nada shugabanni, APC ta ce an tsaida ‘yan takara babu shugabanni
- Alkalai sun tabbatar da cewa babu abin da yake nuna jam’iyyar PDP ta yi wa umarnin kotu biyayya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Kotun daukaka kara ta gabatar da hukunci a shari’ar zaben gwamnan Filato wanda ya gudana a farkon shekarar nan ta 2023.
Leadership ta rahoto cewa Alkalan kotun daukaka kara sun tabbatar da jam’iyyar APC ce ta lashe zaben gwamnan jihar na Filato.
INEC za ta ba APC satifiket a Filato
Mai shari’a Okong Abang ya umarci INEC ta karbe shaidar nasarar da ta ba Caleb Mutfwang wanda yake mulki a karkashin PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan sauraron korafin APC, kotu ta ce Nentawe Yilwatda ne halataccen gwamnan Filato, kwanaki bayan PDP ta tsira da jihar Bauchi.
Gwamnan Filato ya rasa kujerarsa a kotu
Hukuncin da aka zartar a yammacin Lahadin ya na nufin an yi watsi da nasarar da kotun sauraron korafin zabe ta ba PDP da farko.
Abdulaziz Na’ibi wanda ya na cikin magoya bayan Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP ya tabbatar da wannan hukunci a shafin Twitter.
‘Dan siyasar ya nuna jimaminsa kan yadda kujerar ta sullube a hannun PDP ta koma hannun APC wanda ta yi shekaru takwas a mulki.
Yadda APC ta karbe kujerar Gwamnan Filato
Jam’iyyar APC da ‘dan takaranta watau Dr. Nentawe Yilwatda wanda ya zo na biyu sun daukaka kara, sun nemi a tsige Caleb Mutfwang.
A hukuncin da Mai shari’a Abang ya karanto dazu, ya gamsu cewa hujjoji sun nuna PDP ba ta da shugabanni ta tsaida ‘yan takara a Filato.
Majiyar ta ce Kotun ta yarda majalisar gudanarwa ta kasa watau NWC, ba ta da hurumin da za ta tsaida wadanda za su yi takara a jihohi.
Tun da har ba ayi zabe an fitar da shugabannin reshen jiha ba, kotu ta ce a doka, jam’iyyar PDP ba ta da ikon shiga takarar 2023 a Filato.
Elfrieda Oluwayemisi Williams, Dawodu da Okong Abang su ka zartar da hukuncin a yau. Daga nan kuma PDP za ta garzaya zuwa kotun koli.
Kotu ta tsige Gwamna Abba a Kano
Ana da labari jam'iyyar NNPP ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yi a shari'ar zaben gwamnan jihar Kano, an ba APC nasara.
Kotun daukaka karar ta kori karar Abba gida-gida tare da tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin gwamna, za a karasa shari'ar a kotun koli.
Asali: Legit.ng